"Atiku ake So": Jigo a APC Kano Ya Yi Tir da Tikitin Muslim Muslim

"Atiku ake So": Jigo a APC Kano Ya Yi Tir da Tikitin Muslim Muslim

  • Jagora a jam'iyya mai mulki ta APC a Kano, AbdulMajid Dan Bilki Kwamanda, ya ce ba ya goyon bayan tikitin Muslim-Muslim a 2027
  • Ya bayyana hakan duk da jam'iyyarsa ta koma kan tsohon tsarin Muslim Muslim da ya kawo gwamnatin Bola Ahmed Tinubu mulkin a 2023
  • Amma 'dan Bilki Kwamanda ya bayyana cewa wannan magana ce ake yi, amma suna da 'dan takarar da za su tallakara wa mutanen Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Jagora a APC reshen jihar Kano kuma masoyin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya fito karara yana adawa da tsarin Muslim-Muslim a babban zabe mai zuwa.

Ya bayyana haka ne bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince zai ci gaba da tafiya da Kashim Shettima a zaben 2027.

Kara karanta wannan

'Idan Tinubu ya bani kuɗi na shiga APC, zan karba': Ministan Buhari

AbdulMajid dan Bilki Kwamanda ya ce ba za su yi Muslm Muslim ba
Shugaban kasa Bola Tinubu, AbdulMajid dan Bilki Kwamanda Hoto; Bayo Onanuga/AbdulMajid dan Bilki Kwamanda
Source: Facebook

A hira da ya yi da DCL Hausa, AbdulMajid Dan Bilki Kwamanda ya bayyana mutumin da yake ganin yawancin 'yan Arewa ke muradin su zaba a zaben shugaban kasar Najeriya.

An fara samun adawa da tikitin Muslim Muslim

A hirar, AbdulMajid Dan Bilki Kwamanda ya bayyana cewa APC ba ta yi shawara mai kyau ba kan batun tikitin Muslim-Muslim.

Ya bayyana cewa da an so sai a yi shawara a ji ra'ayin mutanen da 'yan Arewa ke son su zaba idan kakar zabe ta kankama.

A kalamansa:

"Babu wani mutum da zai zo ya sake yi mana kuri da tikitin Muslim-Muslim. Kowanene shi, wallahi za mu saba masa a siyasa, mu ci mutuncinsa a siyasa."

Kusa a APC zai tallata Atiku

A ci gaba da hirar, AbdulMajid Dan Bilki Kwamanda ya bayyana cewa a yanzu, hankalin mutanen Arewa ya koma kan zaben Atiku Abubakar da ke takara a ADC.

Kara karanta wannan

Kano APC: 'Ayyukan da za su jawo wa Tinubu ruwan kuri'a a 2027'

Kwamanda ya ce Atiku na ADC za su tallata a 2027
Dan takarar jam'iyyar ADC a lokacin da ya ke karban tuta a Abuja Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

A cewarsa:

"80% na mutanen Arewa Atiku ake so. 80% so ake Atiku ya fito mu jefa masa kuri'a, ba don wani abu ba sai don muna ganin Atiku, duk bala'in da muke ciki a Arewa, idan ya samu dama, in Allah Ya so Ya yarda, zai fitar da mu daga cikin hadarin da ke damunmu."

Ya ce suna ba wa APC talala ne domin su samu dama kuma kada a yanke mata hukunci kai tsaue, sai dai ya ce duk da haka, za su tallata wa jama'a su zabi Atiku Abubakar saboda cancantarsa.

Jigon APC ya yabi Tinubu

A baya, mun ruwaito cewa jigon APC a jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso ya yabawa Shugaha Bola Tinubu kan sake daukar Kashim Shettima a matsayin mataimaki domin tunkarar zaben 2027 tare.

Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana cewa wannan matakin zai kara wa jam'iyyar APC karbuwa da karfi a Arewacin Najeriya kuma zai kara karfafa yiwuwar su ci zaben da za a fafata a shekara mai zuwa.

Ya ce mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya taka muhimmiyar rawa wajen hada kan Arewa da kuma wakiltar Najeriya a duniya saboda haka ya cancanci wannan tafiya da za a ci gaba da yi da shi a APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng