Ahmed Yariman Bakura ya ce zai tsaya takarar Shugaban kasa a 2023
Tsohon gwamnan Zamfara, Ahmad Sani Yarima, ya tabbatar da cewa ya na da burin tsayawa takarar shugaban kasar Najeriya.
Sanata Ahmad Sani Yarima ya bayyana wannan ne a lokacin da ya je yi wa Sheikh Dahiru Usman Bauchi ta’aziyyar rashin Matarsa.
Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rahoto, Ahmed Yariman-Bakura ya shaidawa Manema labarai cewa da shi za a gwabza a 2023.
Tsohon Sanatan ya ce ana matsa masa ya fito, don haka ya ce: “Da yardar Allah, zan yi takarar kujerar (shugaban kasa) a 2023.”
Yarima shi ne gwamnan farar hula na farko a jihar Zamfara, inda ya shafe shekaru takwas a kan mulki kafin ya sauka ya zama Sanata.
KU KARANTA: An yi karin haske game da rade-radin kafa wata Jam'iyya
A cewarsa, idan ya samu mulkin kasar nan, zai yaki talauci, sannan ya samar da aikin yi, tare da gina abubuwan more rayuwa.
“APC ta kafa tarihin fito da ‘Dan takarar shugaban kasa ta hanyar zaben kato-bayan-kato, kuma idan Allah ya so zan shiga zaben.”
“Mutane za su zabi ‘Dan takarar da ya cancanta ne ba wanda ya ke da abin hannu ba. Ba kudi za a duba wajen zaben ba.” Inji Yarima.
Bayan ya bayyana sha’awarsa na tsayawa zaben tsaida gwani na APC, Yarima ya nemi Buhari ya kara kokari kan yaki da talauci.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng