Kotun koli ta kwace kujerar gwamnan Imo, ta damka wa APC

Kotun koli ta kwace kujerar gwamnan Imo, ta damka wa APC

Kotun koli ta kwace kujerar gwamnan Imo, Emeka Ihedioha, dan jam'iyyar PDP tare da tabbatar da Hope Uzodinma, dan jam'iyyar APC a matsayin halastaccen zababben gwamnan jihar.

Kotun, mai alkalai bakwai a karkashin jagorancin alkalin alkakalai na kasa (CJN), Mohammed Tanko, ta ce ba Ihedioha ne halastaccen zababben gwamnan jihar Imo ba.

Babbar kotun, wacce ake wa lakabi da 'daga ke sai Allah ya isa', ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) data karbe shahadar cin zabe daga hannun Ihedioha tare da mika shi ga Uzodinma ba tare da wani bata lokaci ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel