VAT da kudin lantarki za su tashi bayan kudirin tattali arziki ya zama doka
Jim kadan da sa hannu a kan sabon kudirin tattalin arzikin Najeriya, Masana su ga hango cewa harajin da aka saba biya a kasar, za su tashi a bana.
Wani rahoto da aka fitar, ya nuna cewa shigar da kudirin tattalin arzikin a matsayin doka zai kawo gwamnati kudi, sannan aljihun jama’a za su yi kuka.
Ga wasu daga cikin karin harajin da za a gamu da su a wannan shekara ta 2020:
1. VAT da sauransu
Dokar da aka shigo da ita, ta sa harajin da ke kan kayan masarufi ya tashi daga 5% zuwa 7.5%. Haka harajin da ake warewa kudin shiga zai tashi. Haka zalika wannan doka za ta shafi harajin mai, da na shigo-da-fita da kaya da kudin da ake karba na hatimi wajen tura kudi a banki.
KU KARANTA: Mutane 50, 000 su na neman aikin mutum 1, 000 a Legas
2. Wutan lantarki
Wani kari da jama’a za su gani watakila shi ne na wutan latarki. A Watan Afrilun bana ake sa ran sabon tsarin kudin da hukumar NERC da kamfanonin DisCos su ka shigo da shi zai soma aiki.
3. Harajin sadarwa
Akwai yunkurin da ake yi na shigo da harajin 9% na abin da aka kashe wajen sha’anin sadarwa. Za a sa haraji ne ga kudin da ake kashewa wajen aika duk wasu sakanni ta layin salula.
4. Kofofin Gari
Ana kuma tunanin a dawo da harajin da ake karba na kudin shiga kofar gari a kan manyan hanyoyi. Wannan zai taimaka wajen gyara tituna, amma hakan zai iya sa kudin mota ya tashi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng