Gwamnan Jihar Kwara da Buhari sun hadu a fadar shugaban kasa

Gwamnan Jihar Kwara da Buhari sun hadu a fadar shugaban kasa

Mai girma gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq, ya yi zama da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Ranar Litinin, 13 ga Watan Junairu, 2020.

Kamar yadda mu ka samu labari a jiya Litinin, gwamnan ya zauna daga shi ne sai shugaban kasa a ofishin na sa da ke fadar Aso Villa a babban birnin tarayya Abuja.

Gwamnan ya yi wa shugaban kasa bayani game da wasu kalubale da jihar ta tsakiyar Arewacin Najeriya ta ke fuskanta tun bayan da ya karbi mulki a tsakiyar 2019.

“Mai girma Gwamnan ya sanar da shugaban kasa halin da ake ciki musamman a game da sha’anin hanyoyi, ruwan sha, ilmi, da harkar noma a jihar Kwara.”

Mista Rafiu Ajakayea wanda shi ne babban Sakataren yada labarai na jihar Kwara ya bayyanawa ‘Yan jarida abin da wannan muhimmin zama da aka yi ya kunsa.

KU KARANTA: Tsohon Gwamnan Bauchi ya gamu da mugun ji da mugun gani

“Gwamnan ya kuma roki shugaban kasa da ya duba titunan gwamnatin tarayya da ke cikin jihar.”

“Ya kuma fadawa shugaban kasa cewa gwamnatin jiha za ta gina titin Kosubosu-Bode Saadu. Ya kuma yi kira ga shugaban kasa ya ba titunan jihar muhimmanci.”

Ajakaye ya bayyana cewa gwamnan ya na so a gina kwalejin ilmi a jihar tare da kafa hukumar da za ta kula da rugar dabbobi tare da bayyana kokarin da ya ke yi.

Daga cikin irin kokarin da gwamnatin AbdulRazaq ta yi, kamar yadda gwamnan ya fadawa shugaban kasa, shi ne biyan tarin bashin albashin da ta samu a jihar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng