Bayan Rasa Sanata Bayero, Pantami Ya Karbi Tsohon Dan Takarar Gwamna a Tafiyarsa

Bayan Rasa Sanata Bayero, Pantami Ya Karbi Tsohon Dan Takarar Gwamna a Tafiyarsa

  • Jam’iyyar PDP ta sake samun karfi bayan maraba da tsohon ɗan takarar gwamnan SDP a zaɓen 2023 na Gombe
  • Dan siyasar ya bayyana goyon bayansa ga Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ɗan takarar gwamnan PDP a zaɓen Gombe na shekarar 2027
  • PDP ta ce wannan sauyin ya nuna ƙarin amincewar jagororin siyasa da masu ruwa da tsaki da hangen nesan Pantami na ci gaban Gombe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta yi babban kamu a jihar Gombe yayin da ake ta shirye-shiryen siyasar zaben 2027.

Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami shi ne ya karbi dan siyasar awanni kadan bayan rasa Sanata Usman Bayero Nafada da ya yi murabus daga PDP.

Pantami ya karbi tsohon dan takarar gwamna zuwa PDP
Farfesa Isa Ali Pantami, Kelmi J Lazarus da sauran baki a gidansa. Hoto: @ProfIsaPantami.
Source: Twitter

Wakilin Legit Hausa ya samu wannan bayani ne daga shafin babban malamin wanda ya wallafa a shafin X a yau Talata 14 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Tafiyar Pantami ta samu gagarumar nakasu, tsohon sanata ya yi murabus daga PDP

Jam'iyyar ta yi maraba da Mista Kelmi Jacob Lazarus, tsohon ɗan takarar gwamnan jam’iyyar SDP a zaɓen gwamnan Gombe na shekarar 2023.

Jam’iyyar ta ce Lazarus ya yanke shawarar shiga PDP tare da bayyana cikakken goyon bayansa ga Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ɗan takarar gwamnan PDP na zaɓen Gombe da ake shirin yi a shekarar 2027.

PDP ta bayyana cewa wannan ci gaba alama ce ta ƙarin amincewar shugabannin siyasa da sauran masu ruwa da tsaki da hangen nesan Farfesa Pantami.

Tsohon dan takarar gwamna ya koma tafiyar Pantami
Farfesa Isa Ali Pantami a filin jirgin sama. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Yadda tasirin Pantami ke inganta PDP

Wannan sauyi da aka samu na nuna yadda amincewar shugabannin siyasa da masu ruwa da tsaki ke ƙaruwa kan hangen nesan Farfesa Pantami na gina Gombe mai haɗin kai, ci gaba da kuma fifita muradun al'umma.

Sanarwar ta ce:

"Wannan ci gaba na nuna yadda amincewar shugabannin siyasa da masu ruwa da tsaki ke ƙaruwa kan hangen nesan Farfesa Pantami na gina Gombe mai haɗin kai.
"Za mu yi aiki tare, da ci gaba da jajircewa wajen gina makoma mai kyau ta hanyar shugabanci na bai ɗaya, ci gaba mai ɗorewa da kuma ingantaccen mulki."

Kara karanta wannan

Babu sunan Jonathan a ‘yan takaran PDP, Wike ya samu yadda yake so wajen INEC

Jam'iyyar ta ce tana ci gaba da jajircewa wajen gina makoma mai kyau ta hanyar shugabanci na bai ɗaya, ci gaba mai ɗorewa da kuma ingantaccen mulki.

A cewar jam’iyyar, ana ganin Farfesa Pantami a matsayin jagoran da ke da manufar haɗa kan al’umma, inganta walwala da kuma sanya bukatun jama’a a gaba.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa ci gaba da samun sababbin masu goyon baya yana ƙara ƙarfafa burinta na samar da ingantacciyar makoma ga al’ummar Gombe.

Alkawarin da Pantami ya yi ga Kiristoci

Mun ba ku labarin cewa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami da mutanen shi sun ziyarci wani coci a kusa da gidanshi a ranar Lahadi 12 ga watan Yulin 2026 da ta gabata.

Malamin addinin ya bayyana cewa saukin hakkin makwabtaka ya kai shi cocin ba yakin neman zaben gwamna ba.

Pantami ya yi alkawarin za su bada gudumuwarsu wajen ganin an sake gina wanna majami’a da ta kone.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.