Bayan Rasa Takara, an Shawarci Tinubu kan Muhimmancin Bala Wunti a Gwamnatinsa
- Wanda ya nemi takarar gwamnan Bauchi a karkashin APC, Bala Mai Jama'a Wunti na ci gaba da samun goyon bayan matasa
- Wani matashi mai suna Ahmad Gamji ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya ba Dr. Bala Wunti babban mukami saboda gogewa da ƙwarewarsa
- Ya ce basira, gogewa da karɓuwar Dr. Bala Wunti a wajen jama'a sun sa ya cancanci jagoranci domin bunƙasa harkar mai da tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Matasa na ci gaba da goyon bayan wanda ya nemi tikitin takarar gwamnan Bauchi karkashin APC, Dr Bala Mai Jama'a Wunti.
Bala Wunti ya nemi takarar gwamnan Bauchi karkashin APC kafin Mohammed Abdullahi Abubakar ya samu nasarar lashe zaben fitar da gwani.

Source: Facebook
Wani matashi mai suna Ahmad Gamji ya bayyana muhimmancin tafiya da Bala Wunti a wata hira da ya yi da wakilin Legit Hausa.
Wunti: Kiran da matashi ya yi ga Tinubu
Gamji ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi la'akari da bai wa Dr. Bala Wunti wani babban mukami a gwamnatinsa.
Ya bayyana cewa Dr. Bala Wunti na daga cikin gogaggun masana a harkar man fetur, kuma yana da ƙwarewar da za ta taimaka wajen bunƙasa wannan fanni.
Ya ce:
"Cancantarsa, gogewarsa da kuma dinbin basiran da Allah ya ba shi a wannan fanin da kuma karbuwarsa wajen al'umma ya sa muke kiran a tafi da shi.
"Rashin Dr. Bala Wunti a cikin harkarkokin siyasar APC a Bauchi da Nigeria ba karamin kalubale ba ne ga tasirin jam'iyyar APC."

Source: UGC
Gogewar da Wunti ke da shi a rayuwa
Gamji ya ce gogewa, ƙwarewa da dimbin basirar da Allah Ya ba Dr. Bala Wunti sun sa ya cancanci a ba shi damar ci gaba da yi wa ƙasa hidima.
Ana ganin rashin Dr. Bala Wunti a cikin manyan harkokin siyasar APC musamman a Bauchi da ma Najeriya babban gibi ne ga jam'iyyar cewar The Nation.

Kara karanta wannan
Albarkacin Shettima, matasan Arewa sun yi wa Tinubu alkawarin ruwan kuri'u a 2027
Matashin ya bayyana cewa wannan gibi na iya rage tasirin APC idan ba a yi amfani da gogewa da ƙwarewar irin tasa ba.
Gamji ya ce dubban matasa da sauran masu kishin Bauchi da Najeriya sun taɓa roƙon Dr. Bala Wunti ya tsaya takarar gwamna saboda irin amincewar da suke da shi.
Ya ce wannan kira ya samo asali ne daga irin gudummawar da Dr. Bala Wunti ke bayarwa wajen tallafa wa talakawa da shiga rayuwarsu kai tsaye.
A cewarsa, Dr. Bala Wunti ya gina kyakkyawar alaƙa da jama'a ta hanyar ayyukan alheri da kuma kyautata zamantakewa.
Ya kammala da cewa bai wa Dr. Bala Wunti babban mukami zai amfani gwamnatin Tinubu, jam'iyyar APC da kuma ci gaban tattalin arzikin Najeriya.
Matasa sun yi wa Tinubu alkawari saboda Shettima
Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Tinubu ya sake tabbatar da amincewarsa ga Kashim Shettima a matsayin wanda zai yi masa mataimakin shugaban ƙasa a 2027.
Kabiru Garba Kobi, wani shugaban matasan APC ya ce Arewa maso Gabas za ta saka wa Tinubu da ruwan ƙuri'u saboda sake ba Shettima tikiti.
Shugaban matasan ya nemi masu adawa da Shettima su mayar da wuka cikin kube, su haɗa kai domin tabbatar da nasarar Tinubu da APC a 2027.
Asali: Legit.ng
