Ganduje zai gama gina cibiyar maganin cutar daji a Kano a 2020

Ganduje zai gama gina cibiyar maganin cutar daji a Kano a 2020

Mai girma gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya fadi dalilin da ya sa gwamnatinsa ta dage wajen gina asibitin cutar daji.

Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa bincike ya nuna masu jihar Kano ta na cikin inda cutar daji watau kansa ta fi damun Bayin Allah a Najeriya.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce cutar kansar mama da ta halittar namiji ta na damun maza da mata don haka ya kafa cibiyar da za ta kawo sauki.

Wannan cibiya da ake ginawa a Kano za ta yi maganin akalla kashi 90% na cututtukan dajin da mutane ke fama da ita a jihar inji Gwamnan Kano.

“Bari in fadu maku sababbin fara wannan muhimmin aiki. Na farko binciken da mu ka yi a kan mutanen Kano game da cutar daji ya nuna mana kansar halittar ‘Da namiji na damun maza, haka Mata su na fama da cutar kansa mahaifa da ta mama da sauran na’ukan cutar daji.”

KU KARANTA: Mace za ta shugabanci Ma'aikatan Gwamnatin jihar Kano

“Na biyu kuma shi ne mu na so mu toshe tazarar da ke tsakanin Mai kudi da Attajiri ta hanyar kafa gangariyar cibiyar yaki da kansa na farko, wanda Mai kudi da talaka duk za su zo Kano. Za mu kafa asusu ta yadda za a rika dawainiyar marasa galihu a Kano.” Inji Ganduje.

Ganduje ya ce: “Binciken mu ya nuna mana cewa na’urorin da za a kafa, za su yi maganin 90% na matsalolin cutar daji da ake fama da su a jihar Kano.”

Kwamishinan harkar lafiya na Kano, Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa, ya jinjinawa Ganduje da ya fara tunanin wannan aiki wanda za a gama a Yulin bana.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel