2027: Pantami Ya Yi Zargin an Shirya kaiwa Tawagarsa hari a Gombe

2027: Pantami Ya Yi Zargin an Shirya kaiwa Tawagarsa hari a Gombe

  • Sheikh Isa Ali Pantami ya fara ziyarar godiya ga shugabannin PDP a kananan hukumomin Shongom, Kaltungo da Billiri
  • Pantami ya zargi wani jami'i da neman kawo cikas ga shirye-shiryen tafiyarsa domin shirya mugun shiri a kansa da mabiyansa
  • Tsohon ministan ya yi kira ga mabiyansa da kada su ji tsoro, inda ya sanar da shirinsa na zuwa Akko, Balanga da Yamaltu-Deba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Tsohon ministan sadarwa, Isa Ali Pantami, wanda ya bar APC ya shiga PDP don neman kujerar gwamnan jihar Gombe, ya fitar da wata sanarwa mai zafi a ranar Talata, 14 ga Yulin 2026.

Hakan na zuwa ne bayan malamin ya fara zuwa kananan hukumomi domin tattaunawa da shugabannin jam'iyyar PDP a jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Adeyemi: 'Yadda na samo aron N400m wajen kafa hukumar bogi

Sheikh Isa Ali Pantami
Sheikh Isa Ali Pantami yayin ganawa da 'yan APC a Billiri. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

A cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Pantami ya bayyana cewa ziyarar da ya kai wa shugabannin jam'iyya a kananan hukumomin Shongom, Kaltungo da Billiri ta samu karbuwa.

Zargin kaiwa Pantami hari

Sheikh Pantami ya zargi wani mutum, wanda bai ambaci sunansa a fili ba, da neman jerin tarurruka da shirye-shiryen tafiyarsa, inda ya ce:

"Jiya Litinin, mun fara ziyarar godiya tare da ganawa da shugabannin jam’iyyarmu a Ƙananan Hukumomin Shongom, Kaltungo da Billiri.
"Tarbar da aka yi mana ta kasance mai matuƙar armashi, kuma al’ummar ƙananan hukumomin uku sun karɓe mu cikin karamci da girmamawa ta musamman.

Ya cigaba da cewa:

"Ya ga bidiyoyin tarbar da aka yi mana, kuma hakan ya dame shi domin hasashensa ya rushe warwas.
"Saboda haka ya fara neman sanin jadawalin zirga-zirgarmu domin shirya mana makirci. Ta yaya waɗanda suka rantse da Alƙur’ani ko Littafi Mai Tsarki cewa za su kare al’umma za su kasance suna shirya sharri ga mutanen da suke jagoranta?

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa zai ba da ilimi kyauta, a rika ba dalibai abinci

Sheikh Isa Ali Pantami
Sheikh Isa Ali Pantami bayan zuwa filin jirgin sama a Gommbe. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Magana kan yancin zirga-zirga

Malamin ya bayyana cewa dokar kasa ta ba kowane dan Najeriya damar zuwa dukkan wurare ba tare da tsangoma ba.

Ya ce:

"’Yancin zirga-zirga haƙƙi ne da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ba kowane ɗan ƙasa. Sashe na 41(1) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na shekarar 1999 ya tanadi cewa kowane ɗan ƙasa yana da ’yancin yin zirga-zirga cikin ’yanci a ko’ina cikin ƙasar tare da zama a duk inda ya zaɓa.
"Don ya sani, jadawalin tafiyarmu na yau, da yardar Allah, shi ne Ƙananan Hukumomin Akko, Balanga da Yamaltu-Deba.
"Haka kuma mun samu labarin wani shiri na musamman da aka tsara a Akko ta hannun ’yan daba masu alaƙa da wani zaɓaɓɓen jami’in gwamnati (ɗan majalisa)."

Maganar ba mawaka kudi

Baya ga batun kai hari, Sheikh Pantami ya yi zargin cewa ana yi wa magoya bayan shi barazana kan magana da suke game da kudin da aka ce an ba wasu mawaka a jihar.

Kara karanta wannan

Bayan saukar Pantami a filin jirgi, gwamnatin Gombe ta yi barazanar bincike

Sanarwar ta ce:

"An kuma umarci wasu daga cikin magoya bayanmu da su daina magana ko yaɗa bayanai game da makudan kuɗin da aka bai wa mawakan Hausa daga Kano.
"Ta yaya za a iya hana yaɗuwar labarin alhali ɗaya daga cikinsu ya fice daga ƙungiyar kuma ya bayyana gaskiya tare da cikakkun bayanai?
"Muna kira ga shugabannin jam’iyyarmu, magoya bayanmu da dukkan mambobin ƙungiyar Pantamiyya da kada su bari irin waɗannan mugayen shirye-shirye su tsorata su."
"Haka kuma muna kira ga hukumomin gwamnati da abin ya shafa da su sa ido tare da gano waɗanda ke shirya mugunta ga wasu."

Inuwa ya gana da Bayero Nafada

A wani labarin, mun kawo muku cewa jam'iyyar APC ta fara yunkurin janye manyan jam'iyyar PDP domin dakushe nasarar Sheikh Pantami a Gombe.

Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya da dan takarar gwamna na APC a jihar, Jamilu Gwamna sun gana da Sanata Bayero Usman Nafada.

Sanata Bayero Nafada na cikin manyan PDP da suka taba yin takarar gwamna a karkashin jam'iyyar amma bai kai ga nasarar lashe zabe ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng