Kotu Ta Hukunta Mutumin da aka Kama da Laifin Ta'addanci
- Babbar Kotun Tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja ta yanke wa Muhammad Sani hukunci bayan an tabbatar da laifin aikin ta'addanci a Najeriya
- Kotu ta same shi da laifin haɗa baki da kuma ɓoye muhimman bayanai game da fitaccen ɗan bindiga Danranmi, lamarin da ya kai ga aka kama shi
- Kotun ta ce wanda aka yanke wa hukuncin ya san Danranmi na samar da makamai da alburusai ga masu garkuwa da mutane amma ya ja bakinsa ya yi shiru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta yanke wa wani mutum mai suna Muhammad Sani hukuncin dauri a kotu.
Kotu ta daure shi shekara 20 a gidan yari saboda laifin haɗa baki da kuma ɓoye bayanai game da wani fitaccen ɗan bindiga mai suna Danranmi.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa gurfanar da Sani, mazaunin ƙauyen Nabi da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja, kan tuhume-tuhume huɗu da suka shafi laifukan ta'addanci.
Kotu ta daure dan ta'adda
TVC News ta kawo labarin cewa a cikn takardun tuhuma, an gano Sani da Danranmi, wanda har yanzu ake nema ruwa a jallo, sun haɗa baki ne domin ɓoye bayanin a kan Danranmi.
Rahotanni sun ce Danranmi fitaccen ɗan bindiga ne da ke samar da makamai da alburusai ga masu garkuwa da mutane da sauran 'yan bindiga a jihar Neja da kewaye.
An kuma zargi Muhammad Sani da sanin irin ayyukan Danranmi, amma ya ƙi sanar da jami'an tsaro duk da cewa bayanan da yake da su za su taimaka wajen cafke wanda ake zargin bisa dokar hana ta'addanci ta shekarar 2022.
Sauran tuhume-tuhumen ta'addanci
A tuhuma ta uku da ta huɗu, masu gabatar da ƙara sun ce Danranmi ya bai wa Sani kuɗi N580,000 domin sayo harsasai guda 150 daga wani da ake kira "Chairman", duk da cewa yana da dalilin sanin za a yi amfani da su wajen aikata laifukan ta'addanci.

Source: Twitter
Da yake yanke hukunci, Mai Shari'a Emeka Nwite ya daure Muhammad Sani shekara 20 kan tuhuma ta farko da ta biyu ba tare da zabin tara ba.
Alƙalin ya ce hukuncin zai fara aiki ne daga ranar 11 ga Janairun 2023, ranar da aka kama Sani. Kotun ta kuma umarci a tsare shi a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja domin ya cika wa'adin hukuncin da aka yanke masa.
Sojoji sun farmaki yan ta'adda
A baya mun wallafa cewa dakarun rundunar sojoji ta Operation Fansan Yamma sun dakile hare-haren 'yan bindiga a Kaura Namoda da ke jihar Zamfara a lokacin da mutane dauke da makamai suka kai masu hari.
Jami'an tsaron sun yi nasarar kashe Alhaji Tukur, kani ga fitaccen shugaban 'yan bindiga Alhaji Shehu Bagiwaye, sannan rundunar sojin sama ta kai farmaki kan 'yan bindiga kusan 300 da ke kan babura.
A yayin artabun da aka yi tsakanin bangarorin biyu da aka shafe tsawon lokaci ana yi sojojin sun tilasta wa 'yan bindigar tserewa bayan sun yi musu mummunar ɓarna tare da jikkata da dama daga cikinsu.
Asali: Legit.ng

