Rashin aikin yi: Ya kamata a maida hankali kan hukumar NDE - Honarabul Mani

Rashin aikin yi: Ya kamata a maida hankali kan hukumar NDE - Honarabul Mani

Honarabul Aminu Ashiru Mani wanda ke wakiltar Mani da Bindawa a majalisar wakilan tarayya ya yi wata hira da Jaridar Daily Trust kwanan nan.

A wannan hira, ‘Dan majalisar tarayyar na jihar Katsina ya jawo hankalin gwamnatin tarayya ta bada muhimmanci ga hukumar nan ta NDE ta kasa.

Aminu Ashiru Mani ya bayyana cewa wannan hukuma ce ta ke da alhakin horas da Matasa domin su samu abin yi da za su rike kansu a Najeriya.

‘Dan majalisar na jam’iyyar APC mai mulki da rinjaye ya ke cewa idan aka karfafa NDE, za a samu sauki game da masifar talauci da ake fama da shi.

KU KARANTA: Yariman-Bakura ya nemi Buhari ya kara kokari game da rashin aikin yi

Rashin aikin yi: Ya kamata a maida hankali kan hukumar NDE - Honarabul Mani
Aminu Mani ya ce ya kamata a karawa hukumar NDE karfi
Asali: Twitter

Aminu Mani ya yaba da irin kokarin da Darekta Janar na wannan hukuma ta NDE, Dr. Nasir Ladan Mohammed, ya ke yi na sakewa hukumar fasali.

Honarabul Mani ya nuna cewa za a dade ba a manta da aikin Nasir Ladan Mohammed ba saboda gyare-gyaren da ya kawo a cikin kankanin lokaci.

“Yanzu da mu ke da yawan kusan miliyan 200 a kasar nan, hukumar za ta zama silar rage talauci. Mutane su samu hanyar cin abinci, su kama sana’a.”

“NDE za ta taimaka wajen cika alkawuran da mu ka yi. Babbar matsalarmu a kasashen Afrika ita ce talauci, ya za a magance talauci? Samar da abin yi.”

A Najeriya sai mutum ya shafe shekaru 10 bayan ya gama Digiri ba ya aiki. Wannan ya sa Mani ya bada shawarar NYSC ta rika ba Matasa jarin kudi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel