Gwamnonin Jihohin Najeriya da aka yi a 1999 da Ubangiji ya dauki ransu
A wannan karo kuma mun kawo maku jerin wasu tsofaffin gwamnoni ne da aka yi a Najeriya wanda yanzu sun riga mu gidan gaskiya.
Mun tattaro jerin gwamnonin bayan ne tare da takaitawa zuwa ga wadanda su ka yi mulki bayan sake shigowar mulkin farar hula a 1999.
1. Umaru ‘Yaradua
Marigayi Ummaru Musa ‘Yaradua ya bar Duniya ne shekaru 3 bayan ya sauka daga kujerar gwamnan Katsina, har ya zama shugaban kasa. ‘Yaradua ya rasu ne ya na kan mulkin kasa a 2010.
2. DSP Alamieyeseigha
Wannan tsohon gwamna da yanzu aka rasa a Najeriya shi ne Diepreye Solomon Peter Alamieyeseigha wanda ya yi gwamna a Bayelsa. Hawan jini ne ya kashe tsohon gwamnan a 2015.
3. Habubakar Habu Hashidu
Jama’a da dama sun manta da gwamnan jihar Gombe na farko na farar hula watau Abubakar Habu Hashidu. Alhaji Habu Hashidu ya rasu ne a tsakiyar 2018 bayan ya yi fama da rashin lafiya.
KU KARANTA: Gwamnonin da su ka fi shahara a shekarar bara a Najeriya
4. Muhammad Alabi Lawal
Tsohon gwamna Mohamamed Lawal shi ne ya fara riga mu gidan gaskiya daga cikin gwamnonin da su ka hau mulki a 1999. Lawal ya cika ne Nuwamban 2006 bayan wata rashin lafiya a Landan.
5. Abdulkadir Kure
Injiniya Abdulqadir Kure ya na daga cikin tsofaffin gwamnonin da yanzu aka rasa a Najeriya. Kure ya yi gwamna a Neja, sannan Ubangiji ya karbi ransa a kasar waje a farkon shekarar 2017.
6. Abubakar Mala Kachalla
Mala Kachalla wanda ya yi gwamna a jihar Borno daga 1999 zuwa 2003 a karkashin ANPP ya rasu ne a 2007. Kachalla ya sha kasa bayan da ya sauya-sheka ya nemi tazarce a zaben 2003.
7. Prince Abubakar Audu
Marigayi Abubakar Audu ya na cikin wadanda ba za a taba manta yadda mutuwa ta mamayesa ba. Audu ya gamu da mutuwar fuju’a ne yayin da ya ke daf da sake zama gwamnan Kogi a 2015.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng