Sanata Ndume Ya Yi Magana da Tinubu Ya Sake Ɗaukar Musulmi a matsayin Mataimaki a 2027
- Sanata Ali Ndume ya taya Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, murnar sake fitowa a matsayin abokin takarar Bola Tinubu a 2027
- Ndume ya ce matakin da Shugaba Tinubu ya ɗauka ya nuna amincewa da ƙwarewa, biyayya da jajircewar Shettima
- Ya bayyana cewa tikitin Tinubu-Shettima zai ƙara wa APC ƙarfi tare da taimaka wa jam’iyyar samun nasara a babban zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno, Nigeria - Sanata mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu, Muhammad Ali Ndume, ya bayyana farin cikinsa na sake daukar Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Ya ce sake zaɓen mataimakin shugaban ƙasa a matsayin abokin takarar Shugaba Tinubu a zaɓe na gaba zai ƙara wa jam’iyyar APC ƙarfi wajen neman samun nasara.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce Ndume ya bayyana haka ne bayan ya kai wa Shettima ziyara a gidansa domin taya shi murnar sake samun tikitin mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen da ke tafe.
Ali Ndume ya yabawa Bola Tinubu
Sanatan ya ce matakin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka ya nuna hangen nesa, dabarun shugabanci da kuma cikakken amincewa da ƙwarewa, biyayya da sadaukarwar Shettima.
Ya ce:
“Na kai wa Mai Girma Sanata Kashim Shettima ziyara domin taya shi murnar wannan gagarumar nasara da ya samu. Nauyi ne da ya rataya a wuyanmu a matsayinsu na shugabanni da kuma ‘yan jihar Borno mu tsaya tare da namu kuma mu yi masa murna.”
Ndume ya tabbatar da cancantar Shettima
Sanata Ndume ya kuma gode wa Shugaba Bola Tinubu bisa ci gaba da amincewa da Shettima a matsayin abokin takararsa, kamar yadda Leadership ta rahoto.
A cewarsa, gogewa, ƙarfin siyasa da kuma biyayyar da Mataimakin Shugaban Ƙasar ke da ita za su ƙara wa APC damar samun nasara a babban zaɓen 2027.
Ya bayyana Shettima a matsayin shugabn da y dce a dogaro da shi, wanda jajircewarsa wajen yi wa ƙasa hidima da kuma biyayyarsa ga manufofin APC suka ci gaba da ƙarfafa gwiwar mambobin jam’iyyar da sauran ‘yan Najeriya.

Source: Facebook
Sanata Ya yi hasashen nasarar APC
Ndume ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa tikitin Tinubu-Shettima zai taimaka wajen ƙarfafa nasarorin da gwamnatin mai ci ta samu tare da samar wa APC kyakkyawar hanya domin sake samun nasara a zaɓen 2027.
A cewarsa, tikitin Tinubu/Shettima zai sake samun karbuwa a wurin 'yan Najeriya tare da bude hanyar da jam'iyyar APC za ta sake zarcewa kan mulki a zaben da ke tafe.
Kiristoci sun goyi bayan Tinubu/Shettima
A wani labarin, kun ji cewa wata kungiyar Kiristoci a yankin Arewacin Najeriya ta bayyana matsayarta kan sake daukar Kashim Shettima a matsayin mataimaki.
Kungiyar ta yabawa matakin Bola Tinubu na ci gaba da riƙe Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa a zaɓen 2027.
Shugaban kungiyar, Fasto Jolly Usman, ya ce ƙwarewar Shettima da haɗin gwiwarsa da Tinubu sun taimaka wajen inganta tsaro.
Asali: Legit.ng

