Bayan shekaru masu yawa: Buhari ya bayyana dalilin shigarsa siyasa

Bayan shekaru masu yawa: Buhari ya bayyana dalilin shigarsa siyasa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana abinda yasa ya yanke shawarar shiga jam'iyyar siyasa bayan fitowarsa daga kurkuku.

Da yake magana yayin karbar bakuncin matasan jam'iyyar APC da suka ziyarce shi a fadarsa dake Abuja, Buhari ya bayyana cewa ya shiga siyasa ne saboda irin kyakyawar shaidar da ya samu bayan rike mukamin shugaban kasa, gwamnan Borno da kuma ministan man fetur na kasa.

A cewarsa, ya shiga siyasa ne saboda shaidar da ya samu ta kyamatar cin hanci da rasha wa, lamarin da yasa ba a taba samunsa da laifin almundahana da yin sama da fadi da kudi ko kadarorin gwamnati ba a duk mukaman da ya rike.

"An sakeni daga kurkuku saboda ba a sameni da wani laifi ba. Hakan ne yasa na shiga siyasa domin sake hidimta wa kasa cikin mutunci. Na yanke shawarar shiga siyasa domin gwada yin mulki a matsayin farar hula bayan na ajiye kakin soji," a cewar shugaba Buhari.

Da yake magana a kan zangonsa na biyu, shugaba Buhari ya bayar da tabbacin cewa zai kara bayar da himma wajen tabbatar da ganin cewa dukkan 'yan kasa sun ga sakamakon kokarinsa, musamman a bangaren tsaro da kuma farfado da tattalin arzikin kasa da yaki da cin hanci.

"Yanzu ina cikin zangona na biyu a ofis. Nayi rantsuwa da kundin tsarin mulki cewa zan kare Najeriya sannan zan yi duk abinda ya dace domin cigaban kasa," a cewar Buhari.

A nasa jawabin, shugaban matasan jam'iyyar APC, Kwamred Sadiq Shuaibu Abubakar, ya taya shugaba Buhari murnar sake samun nasarar lashe zabe a karo na biyu tare da bashi tabbacin cewa matasa zasu cigaba da bashi goyon baya da gudunmawa.

Abubakar ya bukaci shugaba Buhari da ya kara saka matasa a cikin harkokin gwamnatinsa domin su yi koyi tare da kwaikwayon halayensa na kirki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel