A raba Najeriya kawai idan ‘Yan Arewa su ka nemi su cigaba da mulki – Gbadomosi

A raba Najeriya kawai idan ‘Yan Arewa su ka nemi su cigaba da mulki – Gbadomosi

‘Dan takarar gwamnan jihar Legas a karkashin jam’iyyar ADP a zaben 2019, Babatunde Gbadamosi, ya yi magana game da zabe mai zuwa.

Mista Babatunde Gbadamosi ya ce ya kamata Najeriya ta barke idan har ‘Yan Arewa su ka nemi su ka cigaba da rike kujerar shugaban kasa a 2023.

Babatunde Gbadamosi ya bayyana haka ne a lokacin da ya yi wata doguwar hira da Punch inda ya tattauna game da abubuwan da su ka shafi kasar.

“Idan su ka hakikance, sai mu raba Najeriya, Kowane bangare ya kama hanyar gabansa. Ko ayi wa tsarin kasar talala, ko kuma a bari a barke.”

“Ya danganta ne. Ba na goyon bayan masu cewa babu maganar barka Najeriya a lissafi. Babu abin da mutum ya shirya da ba za a iya canzawa ba.”

KU KARANTA: Sanata Yariman-Bakura ya zai nemi takarar Shugaban kasa a 2023

Hukuncin Ubangiji ne kawai ba a canzawa. Su na nufin hadin-kan Najeriya tamkar wani abu ne da Ubangiji ya saukar da dole mu yi wa biyayya?”

“Idan har tsarin Najeriya ba ya yi wa jama’an kasar aikin da ya kamata, sai mu rabu, kowa ya kama hanyar da za ta fishe shi.” Inji Gbadamosi.

“Masu cewa idan aka rabu za mu yi fama da yunwa, babu komai don mun wahala da yunwa. Yunwar ce ta sa Singapore ta kai inda ta kai a yau.”

Singapore ba ta mai, amma ta na da manyan matatun mai inji ‘Dan siyasar. Wannan ya sa ya ce sai mu barke idan ta kama kamar kasar Rasha.

‘Dan takarar gwamnan ya ce da gan-gan ake hana Ibo mulkin Najeriya, ya ce idan har ba za a ba kowa damar shugabanci ba, sai a raba kasar kawai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel