PDP ta janye dakatarwar da ta yi wa Sanata Sulieman Hunkuy da sauran mutane 6

PDP ta janye dakatarwar da ta yi wa Sanata Sulieman Hunkuy da sauran mutane 6

A ranar Litinin ne jam'iyyar PDP reshen jihar Kaduna ta sanar da janye dakatarwar da ta yi wa tsohon mamba a majlisar dattijai, Sanata Suleiman Hunkuyi, da sauran wasu manyan 'ya'yan jam'iyyar 6.

Sanar da janye dakatarwar ya na kunshe ne a cikin wan jawabi da shugaban riko na jamiyyar PDP a jihar Kaduna, Felix Hayat, ya fitar.

"Jam'iyyar PDP ta janye dalatarwar da ta yi wa Sanata Hunkuyi, Matoh Dogara da Honarabul Ibrahim Lazuru.

"PDP ta na mai bawa Alhaji Imam Lawal da Kanal dauda Albelu Torah shawarar su koma mazabunsu domin sabunta zamansu mambobi a jam'iyyar PDP

"Dakta John Danfulani da Ubale Salmanduna za su iya komawa mazabunsu domin sake yin rijista a matsayin sabbin mambobin jam'iyya, an janye korarsu da aka yi daga cikin jam'iyyar PDP a baya

"Jam'iyya ta na kiran wadanda abin ya shafa a kan su yi amfani da wannan dama da suka samu wajen hada kai da sauran mambobin jam'iyya domin samun hadin kai da cigaban jam'iyyarmu da jiharmu," a cewar Hyat.

PDP ta janye dakatarwar da ta yi wa Sanata Sulieman Hunkuy da sauran mutane 6
Sanata Sulieman Hunkuyi
Asali: Instagram

A ranar 16 g watan Mayu, 2020, Daily Trust ta ruwaito cewa sakataren watsa labaru na jam’iyyar PDP reshen jihar Kaduna, Ibrahim Alberoh Catoh, ne ya fitar da sanarwar dalilan dakatar da su Sanata Hunkuyi.

A cewar sanarwar, PDP ta yi biyayya ga sashi na 57(3) na kundin tsarin mulkinta na shekarar 2017 wajen zartar da wannan hukunci a kan Suleiman Hunkuyi, tsohon Sanata Hunkuyi.

DUBA WANNAN: Batanci ga Annabi: Kotun Kano ta zartar da hukuncin kisa ga matashin mawaki

Sauran sune: Hashir Garba, Mato Dogara, Ibrahim Lazuru, John Danfulani, Lawal Imam Adamu da kuma Ubale Salmanduna. Sai dai PDP ba ta bayyana takamaimen laifin da suka aikata ba.

Amma wasu majiyoyi daga PDP sun ce matakin baya rasa nasaba da shigar da jam’iyyar kara da Hunkuyi yayi jim kadan bayan an kammala zaben shuwagabanni a matakin mazabu.

Sakamakon haka kotu ta bayar da umarni ga jam’iyyar a kan cewa kada ta kuskura ta fitar da sakamakon zaben, wanda ya gudana a ranar 14 ga watan Maris.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel