Wike: APC ta na kutun-kutun domin INEC ta dakatar da zaben Gwamnan Jihar Edo

Wike: APC ta na kutun-kutun domin INEC ta dakatar da zaben Gwamnan Jihar Edo

- Ana musayar kalamai tsakanin PDP da APC a game da zaben Jihar Edo

- Gwamna Nyesom Wike ya ce Jam’iyyar APC ta na shirya magudin zabe

- Jam’iyyar APC ta maidawa Wike martani bayan ya caccaki Oshiomhole

Shugaban yakin neman zaben jam’iyyar PDP a jihar Edo, Gwamna Nyesom Wike, ya zargi jam’iyyar APC da yunkurin dakatar da zaben gwamnan da za ayi.

Nyesom Wike ya ce jam’iyyar APC ba ta shiryawa zaben Satumba ba, don haka ta ke neman yin dabaru domin ganin hukumar INEC ta fasa gudanar da zaben a kan lokaci.

Gwamnan ya ke cewa bayanan da su ka samu ya nuna jam’iyyar APC su na da niyyar tada hankali da kawo hayaniya da nufin jefa jihar Edo a cikin rikicin siyasa.

A cewar gwamnan, dabarar da APC ta ke so ta yi shi ne, ta tsawaita rikici a jihar har ta kai wa’adin gwamna mai-ci, Godwin Obaseki ya cika ba tare da an yi sabon zabe ba.

KU KARANTA: Ana rikici da PDP kan biyan kudin haya a Bayelsa

Jaridar The Nation ta rahoto Wike ya na kira ga ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro su yi amfani da wannan dama wajen goge tambarin da aka yi masu na murde zabe a Najeriya.

A wani 'kaulin, gwamnan na Ribas ya dura kan tsohon shugaban APC, Adams Oshiomhole, ya ce bai da godiyar Ubangiji don haka ya ke yakar Obaseki domin ya cigaba da rike marar jihar.

Gwamnan ya kuma ce shugaban kasa Muhammadu Buhari bai halarci gangamin APC ba, haka zalika bai marawa Osagie Ize-Iyamu baya a matsayin ‘dan takarar jam’iyyar.

Da ta ke maida martani, APC ta bakin John Mayaki, ta ce Wike ya faye surutu a maimakon aikin da ke gabansa, ta zargi Wike da Godwin Obaseki da cin zarafin al’ummarsu.

Mayaki ya kalubalanci Nyesom Wike ya kawo hujjojin da ke nuna jam’iyyar APC ta na shirin yin magudi ko kuma neman a daga zabe. Kawo yanzu PDP ba ta gabatar da wasu hujjoji ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel