Zagaye na biyu: Jerin sabbin tituna biyar da El-Rufa'i zai mayar ma su hannu biyu a cikin Kaduna

Zagaye na biyu: Jerin sabbin tituna biyar da El-Rufa'i zai mayar ma su hannu biyu a cikin Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da fara zamanantar da wasu sabbin titunan cikin birnin Kaduna guda biyar a cigaba da gyaran cikin garin Kaduna zagaye na biyu.

Da ya ke tabbatar da hakan ga manema labarai, shugaban hukumar kula da titunan jihar Kaduna (KADRA), Injiniya Mohammed Lawal Magaji, ya ce an bayar da kwangilar fadada tutunan ga kamfanin 'Ronches Global'.

A karo na farko na gyaran titunan cikin Kaduna da gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i, ya fara a watan Yuli na shekarar 2019, an mayar da tituna bakwai a cikin birnin Kaduna zuwa masu hannu biyu.

Kazalika, an inganta tare da zamanantar da krin wasu tituna 14 da ke cikin kwaryar birnin Kaduna.

An inganta kofar shiga wurin shakatawa na Gamji tare da mayar titunan Katuru, Alkali, da Muhammadu Buhari, zuwa masu hannu biyu, da sauran wasu titunan a zagaye na farko.

Zagaye na biyu: Jerin sabbin tituna biyar da El-Rufa'i zai mayar ma su hannu biyu a cikin Kaduna
Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

"Za mu fara aiki a zagaye na biyu nan bada dadewa ba, mun kammala duk wani aiki a rubuce.

"Za a mayar da dukkan hanyoyin biyar zuwa ma su hannu biyu. Wadannan hanyoyi sune kamar haka; tititin Isa Kaita da ya tashi daga shataletalen 'Millenium City' zuwa sabon titin Alkali Road.

DUBA WANNAN: Kotu ta rushe kafatanin shugabannin jam'iyyar APC a jihar Zamfara

"Akwai titin Waziri Maccido wanda zai bi ta gaban kwalejin 'Zamani' sannan ya hade da titunan Isa Kaita da Rabah," a cewarsa.

Sannan ya cigaba da cewa, "za a mayar da titin da ya tashi daga Katuru ya bi ta Kasuwan Sati zuwa mai hannu biyu, titin zai hade da titin Kwaleji a Unguwr Dosa."

Ya kara da cewa za a fadada titin da ya tashi daga Isa Kaita zuwa titin Surame, sannan a hadeshi zuwa titin filin 'Golf' wanda zai bulle Unguwar Rimi.

Manajan darektan ya kara da cewa za a fadada babban titin da ya tashi daga 'Fly Over' ya bi ta kwanar 'Peugeot' zuw garejin mota na 'Television'.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel