Akwai hannun 'yan siyasa a rashin tsaron arewa - Gwamna Matawalle

Akwai hannun 'yan siyasa a rashin tsaron arewa - Gwamna Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce akwai hannun 'yan siyasa a kalubalen tsaron da su ka dabaibaye kasar nan.

Matawalle ya bayyana hakan ne yayin da ya ke gabatar da jawabi a wani sansanin sojoji na musamman da ke garin Faskari.

"Mu, 'yan siyasa, ya kamata a zarga a kan batun kalubalen rashin tsaro da ya ki karewa a tsakanin jama'armu. A bayyana take cewa wasu 'yan siyasa su na amfani da kalubalen tsaro a kasa domin biyan bukatar kansu.

"Irin wadannan 'yan siyasa ba za su taba yabon rundunar soji ba saboda ta samu nasara a fagen yaki da 'yan ta'adda.

"Amma, nan da nan, za ka ji muryarsu a kafafen yada labarai domin sanar da harin 'yan bindiga da sauran 'yan ta'adda.

"Irin wadannan 'yan siyasa ba su damu da kishin kasa ko jama'a ba, burinsu kawai shine su makale a kan mulki ta kowanne hali," a cewar Matawalle.

Akwai hannun 'yan siyasa a rashin tsaron arewa - Gwamna Matawalle
Gwamna Matawalle
Asali: UGC

Kazalika, ya bayyana cewa ba shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kadai keda alhakin tabbatar da tsaro ba a kasa.

Ya kara da cewa gwamnonin, shugabannin hukumomin tsaro da sauran 'yan kasa ma su kishi su tashi tsaye wajen ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a tsakanin jama'a.

DUBA WANNAN: Batanci ga Annabi: Kotun Kano ta zartar da hukuncin kisa a kan matashin mawaki

A jiya, Litinin, ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri da gwamnoni shida na jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya.

A cewar wakilin gidan talabijin na Channels TV, gaba daya hafsoshin rundunonin tsaro tare da sifeta janar na rundunar 'yan sandan Najeriya na daga cikin mahalarta taron.

Taron na gudana ne bayan da gwamnonin yankin a makon da ya wuce suka zabi gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin shiyyar.

Gwamnonin sun sha alwashin yin hadaka don kawo karshen aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram, sun kuma bukaci gwamnatin tarayya ta karawa rundunar tsaro makamai da sauran kayan aiki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel