Bayelsa: Mai gida ya bukaci PDP ta biya N105m a matsayin bashin kudin hayan shekaru

Bayelsa: Mai gida ya bukaci PDP ta biya N105m a matsayin bashin kudin hayan shekaru

Mai ginin da jam’iyyar PDP ta ke haya a jihar Bayelsa, Mista Chubby Ben-Walson, ya bukaci shugabannin jam’iyyar su biya shi kudin hayar da ya ke binsu.

Chubby Ben-Walson ya nemi jam’iyyar PDP ta reshen Bayelsa ta biya shi wadannan kudi kafin ta tattara ta bar masa gini. Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto a ranar Litinin.

Ben-Walson ya ce jam’iyyar PDP ba ta biya shi kudin hayar da ta ke yi ba har na tsawon shekaru shida, sai kuma kawai ta aiko masa da takarda cewa za ta bar gidan na sa.

Wannan Bawan Allah ya ce ya ba jam’iyyar PDP hayan gininsa bene mai hawa shida ne tun 2008.

A ranar 18 ga watan Yuni, 2020, wani babban kotu da ke zama a garin Yenogoa ya yanke hukuncin cewa jam’iyyar PDP ta biya wannan Mai gida kudinsa Naira miliyan 105.

Alkalin kotun ya ce wannan shi ne bashin da ake bin PDP na zaman da ta yi ta na hayar shagon da ta maida babbar sakatariyar ta a jihar Bayelsa na tsawon shekaru shida.

KU KARANTA: 'Yan siyasan da Obasanjo ya yi wa ritaya a lokacin ya na rike da madafan iko

Mai gida ya bukaci PDP ta biya N105m a matsayin bashin kudin hayan shekaru 6
Gwamnan Bayelsa Sanata Douye Diri
Asali: UGC

Bayan an yanke wannan hukunci, Ben-Walson ya ce wani daga cikin shugabannin PDP ya tunkari Lauyansa a game da yadda za a biya shi bashin kudin hayar.

“Sai kuma shugaban jam’iyya, Solomon Agwana da sakatarensa, Gesiye Isowo, su ka aiko mani takarda cewa za su tattara kayansu su bar ginin, bayan sun yi mani barna.”

“A ce PDP sun ki biya na kudina ya zama rashin tausayi da zalunci; Wannan shi ne ginin da su ka yi shekaru su na aiki a ciki, har su ka samu nasara a zabuka da-dama a Bayelsa.” Inji Ben-Walson.

Da ‘yan jarida su ka tuntubi shugaban jam’iyyar mai mulki a jihar, Solomon Agwana, ya bayyana cewa sun dakatar da hayan da su ke yi a shagon ne domin gudun kudinsu ya karu.

Agwana ya ce jam’iyyar PDP ta daukaka kara bayan ta sha kashi a kotu, duk da haka kuma su na kokarin ganin yadda za su yi sulhu da wannan mutumi ba tare da an je kotu ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel