Kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin INEC, ta dawo da jam'iyyun siyasa 23, za a dangana kotun koli

Kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin INEC, ta dawo da jam'iyyun siyasa 23, za a dangana kotun koli

Wata kotun daukaka kara da ke zama a Abuja ta dawo da jam'iyyun siyasa 23 da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kwace musu rijista.

Wasu daga cikin jam'iyyun da kotu ta dawo da su akwai ACD da PPA.

Kotun ta janye kwace musu rijista ne a hukuncin da ta yanke na ranar Litinin kuma Shugaban kotun daukaka kara, mai shari'a Monica Dongban-Mensem ta sa hannu.

A wani hukunci, kotun ta ce ba shari'a bane, ba kundin tsarin mulki bane kuma ta soke hukuncin babbar kotun tarayya da ta jaddada hukuncin INEC na kwace rijistar wasu jam'iyyun siyasar.

Kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin INEC, ta dawo da jam'iyyun siyasa 23, za a dangana kotun koli
Kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin INEC, ta dawo da jam'iyyun siyasa 23, za a dangana kotun koli Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Alkalai hudu na kotun da suka samu shugabancin mai shari'a Sodipe Lokulo sun jaddada cewa ba a bi tsarin shari'a ba wurin kwace rijistar jam'iyyun.

Kotun ta kara da cewa, hukuncin INEC bai yi biyayya ga sashi 225 na kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999 ba saboda bata bayyana dalilan kwace rijistar ba.

A ranar 6 ga watan Fabrairu, INEC ta sanar da kwace rijistar jam'iyyun siyasa 74 daga cikin 91 na fadin kasar nan.

Ta ce ta yanke wannan hukuncin ne sakamakon yanayin kwazon jam'iyyun da ta duba bayan zaben 2019.

Duk da jam'iyyu 75 ke cikin jerin sunayen, jam'iyyar APP ta samu dokar kotu da ta hana INEC kwace mata rijista.

Hukumar zaben mai zaman kanta tayi dogaro ne da kundin tsarin mulki na 1999 da ya bata karfin ikon kayyade dukkan ayyukan jam'iyyun siyasa.

KU KARANTA KUMA: Jiragen ruwa 18 ke sauke kayayyaki a Legas - NPA

Rashin gamsuwa da wannan ci gaban ne wasu jam'iyyun siyasa suka maka hukumar zaben mai zaman kanta a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Amma a hukuncin watan Yuni na Mai shari'a Taiwo Taiwo, ya jaddada karfin ikon hukumar na kwace rijistar jam'iyyun siyasa a kasar nan.

Amma kuma hukumar zaben mai zaman kanta ta bayyana rashin gamsuwarta da wannan hukuncin na kotun daukaka kara inda ta sha alwashin tunkarar kotun koli.

Kamar yadda ta wallafa a shafinta na twitter, INEC ta ce: "Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) na cikin hukuncin kotun daukaka kara da ta yanke a yau, 10 ga watan Agusta, a cikin wata kara da ACD da wasu jam'iyyu 22 suka daukaka game da kwace musu rijista.

"A hukuncin kotun daukaka kara ta riki cewa kwace wa jam'iyyar ACD da wasu 22 rijista ba ikon hukumar bane sannan ta bukaci a dawo da su.

"Idan za mu tuna, a ranar 289 ga watan Yulin 2020, kotun daukaka kara a Abuja ta tabbatar da karfin ikon INEC na kwace rijistar wasu jam'iyyu wanda jam'iyyar NUP ta shigar da karar.

"Rashin gamsuwa da hakan ne yasa NUP ta sake shigar da daukaka kara duk da akwai wata a gaban kotun koli.

"Hukumar a halin yanzu tana fuskantar hukunci biyu ne mabanbanta da take kalubalanta. Daya na jaddada karfin ikon hukumar wajen kwacewa jam'iyyu rigista, dayan kuwa na soke hana wa ACD da jam'iyyu 22 rijista.

"A saboda haka, hukumar ba za ta karba kowanne hukunci ba sai dai ta garzaya kotun koli don samun gamsasshen hukunci." takardar da INEC ta fitar ta bayyana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel