Ranar Matasa: CENYLON ta zabi Hope Uzodinma Gwamna mai kishin-kasa

Ranar Matasa: CENYLON ta zabi Hope Uzodinma Gwamna mai kishin-kasa

Daga cikin abin da kungiyoyin matasan Najeriya su ka shirya domin murnar zagayowar matasa ta Duniya akwai ba gwamnan jihar Imo kyauta a wannan shekara.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa matasan kasar nan sun zabi gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, a matsayin wanda za su nadawa rawanin ‘dan kishin kasa a bana.

Kungiyar CENYLON mai gamayyar matasan kabilu da-dama daga Arewa, kasar Ibo, yankin Yarbawa, Neja-Delta da kuma tsakiyar Najeriya ce ta zabi Hope Uzodimma.

Wannan kungiya ta Coalition of Ethnic Nationality Youth Leaders of Nigeria, ta ba gwamnan wannan kambu ne saboda irin kokarin da ya ke yi wajen taimakawa matasa.

CENYLON ta kuma yaba da kokarin Hope Uzodinma na kawo zaman lafiya da hadin-kai a kasa. A farkon shekarar nan ta 2020 ne Uzodinma ya zama gwamna bayan hukuncin kotu.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Gwamnoni sun gabatarwa Buhari bukatar neman aron kudi

Ranar Matasa: CENYLON ta zabi Hope Uzodinma Gwamna mai kishin-kasa
Gwamnan Imo Hope Uzodinma
Asali: Twitter

Shugaban kungiyar CENYLON na kasa, Mohammed Salihu Danlami, da kuma darektan ayyuka, Morgan Ocheukwu, ne su ka sa hannu a wannan kyauta da aka ba Uzodinma.

Wannan kyauta da ta fito daga matasan ta shiga hannun ‘yan jarida ne jiya a garin Owerri. An rubutawa Mai girma Sanata Uzodinma wannan kyauta tun a ranar Litinin.

Kamar yadda Salihu Danlami da Morgan Ocheukwu su ka bayyana, matasan kasar sun hadu a kan zabin Uzodinma ne a wani taro na musamman da su ka yi a garin Abuja.

Kwamishinan yada labarai da dabaru na jihar Imo, Declan Emelumba, ya yi karin bayani da cewa kungiyar matasan za ta gabatar da laccar bana ne a kan hadin kai da zaman lafiya.

Su ka ce: “Mun zabi Hope Uzodimma gwamna ‘dan kishin kasa, kuma wanda ya fi maida hankali wajen kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali domin bikin ranar matasan Duniya na 2020.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel