Ondo 2020: Bayan kwanaki 48 a PDP, mataimakin gwamna ya sake barin jam'iyyar
Kasa da kwanaki 48 bayan komawarsa jam'iyyar PDP, mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi, ya yi murabus daga jam'iyyar.
Ajayi ya bar jam'iyyar PDP ne inda ya koma jam'iyyar Zenith Labour Party (ZPL), jaridar The Nation ta ruwaito.
Tuni kwamitin gudanarwa na kasa na jam'iyyar ZPL ta amince masa da ya fito takara a karkashinta.
Ajayi ya ce ya bar jam'iyyar PDP ne saboda yadda da yawan jama'ar jihar Ondo ke kira garesa da ya fito don shugabantarsu.
A yayin bayani ta bakin mai bada shawara a kan yada labarai na mataimakin gwamnan, Allen Sowore, ya ce Ajayi ya bukaci magoya bayan sa da su mayar da hankali don nan babu jimawa zai sanar da matakinsa na gaba
Ya jinjinawa shugabancin jam'iyyar PDP na kasa da mambobinsu a kan yadda suka karbesa a takaitaccen lokacin da ya shiga jam'iyyar.
Shugaban jam'iyyar PDP na gundumar Apoi ta II da ke karamar hukumar Ese-Odo, Festus Oboro, ya sanar da cewa ya samu wasikar barin jam'iyyar da Agboola ya aike da ita.
KU KARANTA KUMA: Sauyin-shekar Dogara ya birkita lissafin shugabancin Majalisa
Ajayi ya bar jam'iyyar APC kuma ya koma PDP a ranar 21 ga watan Yunin 2020.
Rashin samun tikitin takarar gwamnan karkashin jam'iyyar ne yasa ya koma ZPL.
A gefe guda, mun ji cewa alamu sun nuna cewa samun nasarar Eyitayo Jegede a matsayin ‘dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Ondo bai yi wa wasu ‘yan takara dadi ba.
Jaridar Daily Trust ta ce samun tikitin da Eyitayo Jegede ya yi, ya keta jam’iyyar PDP. Jegede ya yi galaba ne a kan wasu ‘yan takara bakwai har da mataimakin gwamna.
Tsohon kwamishinan shari’an na Ondo ya karbi satifiket a matsayin wanda zai rikewa PDP tuta a zaben Ondo. Jegede ya karbi takardar shaidan nasara ne a sakatariyar jam’iyyar.
Da ake mikawa Mista Eyitayo Jegede satifiket, mutum guda ne rak cikin wadanda su ka nemi takara ya yi masa rakiya, wannan ba kowa ba ne face Godday Erewa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng