Gwamna El-Rufai ya nada Shugabannin Ma’aikatu da Hukumomi a Kaduna

Gwamna El-Rufai ya nada Shugabannin Ma’aikatu da Hukumomi a Kaduna

A ranar Litinin, 10 ga watan Agusta, 2020, aka bada sanarwar cewa Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi nadin wasu sababbin mukamai.

Nadin mukaman da aka yi sun hada da shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamantin jihar, wanda za su taimakawa gwamnatin Malam Nasir El-Rufai.

Jawabin da ya fito daga bakin Hadimin gwamnan a kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya ce an nada shugabannin da za su rika sa ido a KADIRS.

Jeremiah Adams, Mohammed Lawal da Simeon Kato sun zama manyan Darektoci a karkashin hukumar KADIRS mai alhakin tara haraji a jihar Kaduna.

Aysha Mohammed za ta rike kujerar sakatariyar hukumar KADIRS, kuma mai bada shawara a kan harkokin shari’a. Za su yi aiki tare da shugaban KADIRS, Dr. Zaid Abubakar.

KU KARANTA: Ba a ba Musulmai kujeru da mukamai a Jihar Taraba

Gwamna El-Rufai ya nada Shugabannin Ma’aikatu da Hukumomi a Kaduna
Nasir El-Rufai Hoto: Twitter
Asali: UGC

Haka zalika mai girma gwamna Nasir El-Rufai ya nada Ishaya Anka a matsayin shugaban hukumar da ke kula da ma’aikatan kananan hukumomi.

Wakilan da aka zaba daga kowane bangare na jihar a karkashin wannan hukuma ta ma'aikata su ne: Magaji Sadiq, Mahmud Zailani da kuma Cecilia Musa.

Hukumar dillacin labarai na kasa ta ce an nada Dan Ndackson a matsayin shugaban hukumar fansho ta jihar. Farfesa Salamatu Isah ce sabuwar sakatariyar hukumar.

Dr. Zayyad Tsiga ya zama shugaban hukumar da ke kula da rajistar mazauna jihar. Shi kuma Abdullahi Bayero shi ne manajan ma’aikatar cigaban harkar noma ta KADP.

Dr. Usman Ahmed Danbaba ya shiga cikin masu ba mai girma gwamna Nasir El-Rufai shawara. Sauran wadanda aka ba mukami su ne Sulaiman Tahir da kuma Mustapha Shittu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel