Ka bada damar maye gurbin Dogara - PDP ga Gbajabiamila

Ka bada damar maye gurbin Dogara - PDP ga Gbajabiamila

- Jam'iyyar PDP ta nemi kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya bada damar maye gurbin Yakubu Dogara wanda ya bar jam'iyyar zuwa APC

- PDP ta ce bukatarta ta ci karo da wasu tarin dokokin na kundin tsarin Najeriya wanda ya bukaci da a bada damar maye gurbinsa a cikin kwanaki 7 da samun wasikar

- A yanzu haka magoya bayan tsohon kakakin majalisar wakilan da dama sun mara masa baya zuwa APC

- Har ila yau wani dan gaba-gaba a takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben karamar hukuma mai zuwa a in Bogoro, Bulus Iliya ya bi Dogara

Jam'iyyar PDP reshen jihar Bauchi, ta bukaci kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da ya bada damar maye gurbin Yakubu Dogara wanda ya barta zuwa APC.

Wasikar mai taken 'bukata daukar matakin shari'a wacce S. Rabo Esq da wasu suka mika ga kakakin majalisar.'

Wasikar ta ce: "Muna rubuta wannan wasikar ne a matsayinmu na wakilan jam'iyyar PDP a fannin shari'a.

"Wacce muke karewa ta sanar da mu cewa Yakubu Dogara, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Tarawa Balewa, Dass da Bogoro a matakin tarayya ya sauya shekar zuwa jam'iyyar APC."

Ka bada damar maye gurbin Dogara - PDP ga Gbajabiamila
Ka bada damar maye gurbin Dogara - PDP ga Gbajabiamila Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Wasikar ta kara da cewa, "wannan ya ci karo da wasu tarin dokokin na kundin tsarin Najeriya wanda ya bukaci da a bada damar maye gurbinsa a cikin kwanaki 7 da samun wasikar nan."

A halin da ake ciki, wani dan gaba-gaba a takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben karamar hukuma mai zuwa a in Bogoro, Bulus Iliya da tarin magoya bayan tsohon kakakin majalisar wakilan, sun koma APC.

KU KARANTA KUMA: Tarbiya tayi wahala, 'yan damfarar yanar gizo sun zama madubin dubawa - Diezani

A yayin karbar masu sauya shekar a Bogoro, shugaban APC na karamar hukumar, Haruna Rikaya, ya ce jam'iyyar na matukar farin cikin karbar 'yan jam'iyyar PDP 6,000.

Shugaban masu sauya shekar kuma dan takarar kujerar shugaban karamar hukumar Bogoro, Bulus Iliya, ya ce ya yanke shawarar komawa APC ne saboda bukatar hadewa da ubangidansa a fannin siyasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel