Talakawa na da ikon canja kowacce gwamnati, amma fa idan sunyi aiki da hankali

Talakawa na da ikon canja kowacce gwamnati, amma fa idan sunyi aiki da hankali

- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana cewa 'yan Najeriya na da damar sauya gwamnati a lokacin da suka so

- Sai dai Lamido ya ce mai zabe na da damar yin duk abinda yaso da damarsa

- Ya kuma ce mai zabe na da damar zama wawa

Alhaji Sule Lamido ya bayyana cewa 'yan Najeriya na da damar sauya gwamnati a lokacin da suka so, amma ya ce mai zabe na da damar yin duk abinda yaso da damarsa.

Ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da Vanguard, yayin amsa tambaya dangane da babbar jam'iyyar hamayya ta APC a jiharsa ta Jigawa.

Lamido ya taba zama ministan harkokin waje a karkashin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya kuma yi gwamna sau biyu, sannan daga bisani ya nemi zama shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP.

Talakawa na da ikon canja kowacce gwamnati, amma fa idan sunyi aiki da hankali
Talakawa na da ikon canja kowacce gwamnati, amma fa idan sunyi aiki da hankali Hoto: PremiumTimes
Asali: UGC

A tattaunawar da aka wallafa a ranar Lahadi, Lamido ya sanar da Vanguard cewa: "Jama'ar kasar nan suna da damar sauya gwamnati a lokacin da suka so.

"Wannan damar tasu ce. Don haka kana da damar zama wawa. Bai kamata mutum ya yi nadama ba a siyasa saboda yana da damar nada gwamnati ko kuma kin yin hakan.

"A don haka idan jama'ar Najeriya suka fada wa farfagandar APC na cewa shekaru 16 da PDP tayi sata kawai take yi, duk da sabbin filayen jiragen sama da suka yi a Kano, Enugu, da sauran jihohi, hakan zai zama abun takaici."

A kan farfadowar APC, Sule Lamido ya ce "APC bata da wani tsari. Abinda suka sani shine sharri. Sun saka 'yan Najeriya cikin mawuyacin hali. Don haka yanzu ya rage ga jama'a da su yi zabinsu."

KU KARANTA KUMA: Ondo 2020: Bayan kwanaki 48 a PDP, mataimakin gwamna ya sake barin jam'iyyar

"Idan da PDP bata hadu da APC ba don samun goyon baya, da ba za su ci zaben 2015 ba.

"Ku tuna zabukan 1999, 2003, 2007 da 2011, da za a hada dukkan jam'iyyun siyasa, basu isa su yi nasara a kan PDP ba," Sule Lamido ya kara da cewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng