Yaki Ya Yi Zafi, Iran Ta Kai Mummunan Harin Ban Mamaki kan Amurka

Yaki Ya Yi Zafi, Iran Ta Kai Mummunan Harin Ban Mamaki kan Amurka

  • Sabon fada ya barke tsakanin Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran inda aka yi musayar hare-hare masu zafi
  • Tun da farko Amurka ta kai hare-hare a Iran bayan da dakarun rundunar IRGC suka farmaki wani jirgin ruwan kasuwanci a mashigar Hormuz
  • Rundunar IRGC ta mayar da martani cikin gaggawa inda ta kai zafafan hare-hare kan wasu sansanonin sojojin Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta yi ikirarin cewa ta kai wani "mummunan hari kuma na ba-zata" hari kan wuraren da Amurka ke amfani da su a Oman.

IRGC ta yi ikirarin kai hari kan wuraren tallafin kayan aiki da wuraren loda man fetur da jiragen ruwan yakin Amurka masu daukar jiragen sama ke amfani da su a tashar jiragen ruwa ta Duqm da ke kasar Oman.

Kara karanta wannan

Yaƙin Amurka da ƙasar musulunci ta Iran ya zama 'alheri' ga attajirin Najeriya, Dangote

Iran ta farmaki sansanonin sojojin Amurka
Makami mai linzami na Iran Hoto: @Iran_military
Source: Twitter

Tashar Aljazeera ta ce kafar yada labaran gwamnatin Iran ta IRIB ta ruwaito cewa sashen hulda da jama'a na IRGC ya sanar da hakan a ranar Lahadi, 12 ga watan Yulin 2026.

Sanarwar ta rundunar IRGC ta bayyana cewa an samu nasarar "lalata" wuraren da aka kai wa harin.

Hari kan sansanin Jordan

Hakazalika, rundunar IRGC ta ce ta kai hari kan wani sansanin sojojin Amurka da ke kasar Jordan.

Rundunar ta yi ikirarin cewa ta lalata cibiyar bada umarni da sarrafawa tare da wurin da ake ajiye jiragen yaki marasa matuka na MQ-9 a sansanin Prince Hassan Air Base, a matsayin martani ga hare-haren Amurka.

A cikin wata sanarwa da sashen hulda da jama'a na IRGC ya fitar, rundunar ta zargi Amurka da kokarin "tilasta ra'ayinta" kan Oman ta hanyar karfafa wasu jiragen ruwa su bi wata "haramtacciyar hanya" ta Kudancin mashigar Hormuz.

Rundunar IRGC ta bayyana cewa sojojin ruwan Iran sun mayar da martani cikin gaggawa kan wannan yunkuri, tashar Anadolu Ajansi ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

An kuma samun matsala a shari'ar da aka nemi ƙwace kadarorin Malami a Abuja

Iran ta zargi Amurka da kai farmakin sama

Rundunar IRGC ta kuma yi ikirarin cewa daga baya sojojin Amurka sun kai hare-haren sama. Sanarwar ta ce:

"Sojojin Amurka masu kashe yara, domin boye gazawarsu, sun kai hare-haren sama kan wasu sansanonin bakin teku da hasumiyoyin sadarwa da ke gabar tekun kudanci. Kamar yadda muka yi alkawari, nan take suka fuskanci mummunan martani kan wannan ta'addanci."

Rundunar ta ce daga nan ne rundunar sojojin sama ta IRGC ta fara aiwatar da matakin farko na ramuwar gayya kan wuraren sojojin Amurka.

"A matakin farko na wannan martani, an kai hare-hare da makamai masu linzami kan muhimman cibiyoyin soja da kayayyakin aiki a sansanin Prince Hassan Air Base da ke Jordan, inda aka lalata cibiyar bada umarni da kuma wurin ajiye jiragen MQ-9." In ji sanarwar
Sojojin Iran sun kai hari kan Amurka
Wasu dakarun sojojin Iran na atisaye Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta yi barazana da karin martani

IRGC ta gargadi cewa duk wani ci gaba da hare-haren da ta kira na "gwamnatin Amurka mai cin amana" zai haifar da martani mafi tsanani daga Iran.

Kara karanta wannan

Iran ta nuna yatsa ga Donald Trump, ta harba makamai kan Kuwait da wasu kasashe 2

A nata bangaren, Amurka ta kai zagaye na uku na hare-hare kan wuraren na'urorin sanya ido, makamai masu linzami da wuraren jiragen yaki marasa matuki a Kudancin Iran.

Rahotanni sun ce hare-haren sun biyo bayan bude wuta da Iran ta yi kan wasu jiragen ruwa na kasuwanci a mashigar Hormuz da kuma sanar da rufe mashigar ruwan har zuwa wani lokaci da ba a bayyana ba.

Sakon Khamenei ga Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa sabon jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei, ya yi alƙawarin ɗaukar fansar mutuwar mahaifinsa, marigayi Ayatollah Ali Khamenei.

Ya ce ɗaukar fansa shi ne muradin al'ummar Iran, yana mai ƙara da cewa nan ba da jimawa ba mutane masu son 'yanci za su aiwatar da wannan aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng