APC: Yankin kudu maso yamma ta jinjinawa El-Rufai a kan kiran komawar mulki wurinsu

APC: Yankin kudu maso yamma ta jinjinawa El-Rufai a kan kiran komawar mulki wurinsu

- Jam'iyyar APC reshen kudu maso yamma ta jinjinawa Gwamna El-Rufai a kan cewa da yayi mulkin Najeriya ya koma yankin a 2023

- Sakataren jam'iyyar a yankin ya ce za su ci gaba da duba irin wadannan muryoyin da ke bata goyon baya har sai ta ga cikar burinta

- Ya ce suna da 'yan siyasa maza da mata da za su iya rike Najeriya yadda ya kamata a 2023

Jam'iyyar APC ta yankin kudu maso yamma ta jinjinawa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a kan cewa da yayi mulkin Najeriya ya koma yankin a 2023.

Ta ce irin wannan kira ne tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya yi, jaridar The Nation ta ruwaito.

Sakataren yada labarai Karounwi Oladapo, a wata takarda da ya fitar, ya ce jam'iyyar APC ta yankin kudu maso yamma za ta ci gaba da duban irin wadannan muryoyin da ke bata goyon baya har sai ta ga cikar burinta.

KU KARANTA KUMA: Ajali: Sauran sa'o'i kadan aurensa, ango ya yi mummunan hatsari

APC: Yankin kudu maso yamma ta jinjinawa El-Rufai a kan kiran komawar mulki wurinsu
APC: Yankin kudu maso yamma ta jinjinawa El-Rufai a kan kiran komawar mulki wurinsu Hoto: The Nation
Asali: UGC

Ya ce: "muna goyon bayan sauran 'yan arewa da za su fito su yi magana kuma a ji su. Babu wani shugaba a arewa da ya bukaci mulkin kasa ya koma kudu da aka ci wa zarafi.

"Tattaruwar ra'ayin shugabannin arewa a kan mulkin kasa ya koma kudu zai cimma nasara kafin zuwan 2023.

"Gwamna El-Rufai ya fara maganar ne a watan Fabrairu amma bata dauki hankali ba saboda ta bayyana ne tamkar jawabin siyasa."

Amma kuma, a wata tattaunawa da aka yi da shi a ranar Lahadi, 9 ga watan Augusta, inda ya sake jaddada goyon bayansa a kan komawar shugabanci kudu, ya samu jinjina.

"Mun kuma ji zantuka a kan komawar mulki Kudu daga bakin Sanata Mohammed Ali Ndume daga Borno. Shugabannin APC na kudu maso yamma na godiya ga Mallam Mamman Daura.

"Muna da 'yan siyasa maza da mata da za su iya rike Najeriya yadda ya kamata a 2023.

"Yankin kudu maso yamma tana sanar da 'yan Najeriya cewa za ta yi kokari. Kira ga irin wannan shugabancin na bayyana kishin kasa. Hadin kai da daidaituwar Najeriya za ta zo ne kafin bukatar kowa.

"Babu shakka za a yi mulkin ne ta hanyar adalci da daidaituwa tare da zaman lafiya."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel