An Ji Dalilan da Suka Jawo Shugaban Karamar Hukuma Ya Yi Murabus, Ya Bar APC a Sokoto
- Shugaban ƙaramar hukuma a jihar Sakkwato ya sanar da cewa ya hakura da ci gaba da rike kujerar da ya ke kai, tare da mika takardar ajiye aiki
- Isa Kalanjeni wanda ke shugabancin karamar hukumar Tangaza da kansa ne ya yi murabus daga kujerar, sannan ya bayyana cewa ya fice daga APC
- Duk da ya sanar da dalilinsa na hakura da APC da kujerarsa, gwamnatin jihar Sakkwato ba ta fitar da sanarwa game da wannan gagarumin sauyi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto – Shugaban ƙaramar hukumar Tangaza a jihar Sakkwato, Isa Kalanjeni, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC mai mulki.
Ba barin jam'iyyar APC kawai ya yi ba, shugaban ya kuma muka takardar murabus daga kujerar shugaban karamar hukumar Tangaza da ya ke jagoranta.

Source: UGC
Jaridar Punch ta kawo labarin cewa Kalanjeni ya bayyana matakan ne a cikin wasiƙu biyu daban-daban da aka miƙa wa hukumomin da abin ya shafa, kuma daga baya suka isa hannun manema labarai a Sakkwato.
Shugaban karamar hukuma ya bar APC
A ruwayar Nigerian Tribune, Isa Kalanjeni ya rubuta wasiƙarsa ta farko mai ɗauke da kwanan watan 5 ga Mayu, 2026, wacce ya aika wa shugaban APC na mazabar Kalanjeni da ke ƙaramar hukumar Tangaza.
A cikin wannan wasika, ya sanar da cewa ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki tare da bayyana dalilan da suka sa ya dauki matakin.
Isa Kalanjeniya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne saboda wasu dalilai na kansa, tare da gode wa jam'iyyar bisa damar da ta ba shi na kasancewa cikinta tsawon lokacin da ya yi.
Sakkwato: Shugaban karamar hukuma ya yi murabus
A wata wasiƙa ta daban mai kwanan watan 7 ga Yulin 2026, wacce aka aika wa Sakataren gwamnatin jihar Sakkwato da Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Kalanjeni ya sanar da yin murabus daga muƙaminsa.
A cikin wasiƙar, ya ce murabus ɗin daga kujerar zababben shugaban karamar hukumar Tangaza zai fara aiki ne nan take daga ranar da ya rubuta wasiƙar.

Source: Facebook
Kalanjeni ya bayyana cewa bai yanke wannan hukunci cikin gaggawa ba, domin ya ce sai da ya tattauna da iyalansa, manyan abokan siyasarsa da kuma masu ruwa da tsaki a al'ummarsa kafin ya cimma matsayar.
Ya kuma bayyana cewa wasu ƙalubalen gudanarwa da suka taso a baya-bayan nan sun sa ba zai iya ci gaba da sauke nauyin da ke kansa yadda ya kamata ba.
A cewarsa, matsalolin sun hana shi gudanar da ayyukan ofishinsa yadda jama'a ke tsammani, lamarin da ya sa ya ga ya dace ya sauka daga muƙamin.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, gwamnatin jihar Sokoto da shugabannin jam'iyyar APC a jihar ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan ficewar Kalanjeni daga jam'iyyar da kuma murabus ba.
Dan takara ya koma APC a Sakkwato
A wani labarin, kun ji cewa dan takarar gwamna ƙarƙashin jam'iyyar PDP a Sakkwato ya fice daga cikinta zuwa APC mai mulki a jihar tare da danganta matakin da jagorancin Sanata Aliyu Wamakko da ayyukan Gwamna Ahmed Aliyu ke yi.
An karɓi tsohon ɗan takarar gwamna a gidan Wamakko da ke babban birnin tarayya Abuja, inda APC ta ce sauyin ya nuna jam'iyyar na ƙara samun karɓuwa a jihar Sakkwato saboda ayyukan da ake yi a Najeriya.
Tsohon Kwamishinan Kuɗi kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Sokoto a zamanin Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa shugabannin siyasa na ci gaba da amincewa da jagoranci da manufofin jam'iyyar.
Asali: Legit.ng


