Sauyin-shekar Dogara ya birkita lissafin shugabancin Majalisa

Sauyin-shekar Dogara ya birkita lissafin shugabancin Majalisa

Sauya shekar tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara zuwa jam'iyyar APC daga PDP ya birkita lissafin shugabancin majalisar wakilai, jaridar Tribune ta ruwaito.

Duk da yadda sauya shekar ta zo a ba-zata ga mutane da yawa, bayanai sun nuna cewa, ya shirya hakan.

Tribune ta gano cewa, a ranar Laraban makon sallah, wasu 'yan jam'iyyar adawa sun samu wani tsohon mataimakin shugaban APC tare da Dogara a Wuse 2 da ke Abuja.

Sauya shekar da amfaninsa ne ya mamaye hirarsu, kamar yadda majiya daga jam'iyyar ta tabbatar.

Majiyar ta tabbatar da cewa sauya shekar Dogara ya biyo bayan son takarar da yake yi tare da Sanata Bola Tinubu, ta ce a bangaren fadar shugaban kasar, ana kokarin boye hakan.

Sauyin-shekar Dogara ya birkita lissafin shugabancin Majalisa
Sauyin-shekar Dogara ya birkita lissafin shugabancin Majalisa Hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: UGC

Majiyar ta ce wannan kokarin tsara shugabancin an yi shi ne a sirrance don ba kowa ne ya sani ba.

Bayan kwanaki biyu da wannan taron, kusan 'yan majalisar biyar tare da Dogara sun samu zantawa da shugaban rikon kwarya na jam'iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni a Abuja.

Majiyar ta tabbatar da cewa, baya ga Gwamna Samuel Otom, wanda ya tabbatar da cewa ana bashi goron gayyata zuwa APC, wani gwamna ya fara tunanin barin PDP din duka.

A makon da ya gabata ne Gwamna Ortom, ya bayyana cewa ana takura masa a kan ya bar jam'iyyar PDP.

Ya nemi zarcewarsa karkashin babban jam'iyyar adawa bayan rikicin da ya barke tsakaninsa da fadar shugaban kasa a kan makiyaya da ke jihar.

KU KARANTA KUMA: Jerin 'yan siyasa 4 da Obasanjo ya disashesu a Najeriya

Wani gwamnan ya bayyana cewa, wani makusancin Bokola Saraki na kokarin komawa jam'iyyar mai mulki.

Ya koma PDP ne tare da uban gidansa amma yanzu babu tabbacin ko akwai wani abinda yasa yake son komawa.

Maimakon mayar da hankali ga sasancin cikin gida kan rigimar da jam’iyyar mai mulki ta riski kanta, an tattaro cewa tawagar Buni ta yanke hukuncin mayar da hankali sosai wajen zawarcin manyan masu sauya sheka daga PDP.

Tana kuma son cimma hakan kafin babban taronta na kasa baki daya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel