Idan aka karbe PDP daga hannun Gwamna Ben Ayade, to za mu bar ta inji Fani-Kayode

Idan aka karbe PDP daga hannun Gwamna Ben Ayade, to za mu bar ta inji Fani-Kayode

- Cif Femi-Fani Kayode ya koka da abin da ke faruwa da PDP a Jihar Kuros Ribas

- ‘Dan siyasar ya soki shirin karbe jam’iyyar PDP daga hannun Gwamna Ben Ayade

- Ya ce muddin aka yi haka, shi da wasu ‘Ya ‘yan Jam’iyya za su fice su bar PDP

Tsohon ministan harkokin jirgin saman Najeriya, Femi-Fani Kayode, ya soki shirin da uwar jam’iyyarsu ta ke yi na karbe PDP daga hannun gwamna Ben Ayade.

Mista Femi-Fani Kayode ya yi wannan jawabi ne a kan shafinsa na Facebook da Twitter, ya na Allah-wadai da yunkurin cin mutuncin da ake yi wa gwamnan jihar Kuros Riba a PDP.

A cewarsa, idan har ba a dauki matakin gyara ba, shi da wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar za su iya barin PDP.

Ya ce: “Zai zama babban kuskure idan majalisar NWC ta PDP ta bari aka karbe jam’iyya a jiharsa daga hannun gwamnan Kuros-Riba, Ben Ayade, aka mikawa wani dabam.”

“Idan har aka yi haka, kuma Ayade ya bar jam’iyyar, a sani cewa babu shakka wasu da-dama daga cikinmu za su fice tare da shi.” Inji Femi-Fani Kayode.

KU KARANTA: Fani-Kayode: Nadin sarautar Sadaukin Shinkafi ta na neman kawo matsala

Idan aka karbe PDP daga hannun Gwamna Ben Ayade, to za mu bar ta inji Fani-Kayode
Femi Fani-Kayode
Asali: Twitter

Femi-Fani Kayode wanda aka fi sani da FFK, ya ce: “Ba za ku wulakanta gwamna mai-ci ko ku yi kokarin ci masa mutunci a jiharsa, a gaban al’ummarsa ba.”

“Wasu daga cikinmu da mu ke goyon bayan wannan shirme, ba za su bari a taba yi masu haka a jihohinsu ba. Kukan kurciya jawabi ne, mai hankali ya ke ganewa.”

FFK ya ke cewa rigimar taba Ayade za ta shafi sauran bangarorin kasar, don haka ya ba masu wannan tunani shawarar su ajiye kayan fadansu ko wasu su sauya-sheka.

“Babu wanda ya isa, ko wanene shi kuma komai karfinsa, ya yi tunanin cewa PDP ta sa ce.:

"Idan aka yi kokarin maida Ayade ba kowa ba, wannan zai jawo rikicin da zai barka jam’iyyar ta ko ina, kuma rigimar ba za ta tsaya a jihar Kuros-Ribas ba.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel