Siyasar Arewa
Kungiyar Kiristoci ta Arewa ta bukaci karin manyan mukamai a gwamnatin Bola Tinubu inda ta yaba da tsarin hada kan kowa, amma ta nemi karin wakilcin Kiristoci.
Jigon APC kuma dan gwagwarmaya a jihar Taraba, Rikwense Muri, ya ki karbar muƙami da Gwamna Agbu Kefas ya yi masa a matsayin hadimi na musamman kan ayyuka.
Bayan Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau ya gana da Bola Tinubu a Lagos, kungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya ta sake gayyatar gwamnan ya fice daga PDP.
Sunny Moniedafe ya shigar da ƙara a kotu kan APC, yana neman jam'iyyar ta mayar masa da N10m da ya biya na fom ɗin takara a 2022, da kuma diyyar N100m.
Sheikh Murtala Bello Asada ya koka kan salon mulkin Bola Tinubu inda ya yi addu'ar Allah ya tarwatsa azzaluman shugabanni da ke lalata yankin Arewa.
Majalisar dokokin Legas ta tsige Mudashiru Obasa saboda zargin rashin ɗa'a. Legit Hausa ta jero shugabannin majalisar jihohi da aka taba tsigewa.
Gwamnatin Bauchi ta zargi shugaba Bola Tinubu da amfani da ministoci domin ruguza 'yan adawa a zaben 2027. Bala Mohammed ya karyata zargin Yusuf Tuggar.
Goyon bayan Isah Liman Kantigi ga Gwamna Bago a 2027 ya jawo cece-kuce. Jam'iyyar PDP ta sha alwashin daukar matakan ladabartar da dan takarar na ta.
Tsohon gwamnan jihar Sokoto a Najeriya, Dalhatu Attahiru Bafarawa, ya sanar da ficewar shi daga babbar jam'iyyar adawa ta ƙasar - PDP. Tsohon gwamnan ya fadi dalili.
Siyasar Arewa
Samu kari