Bello Turji Ya ba Najeriya Zabin Yaki ko Zaman Lafiya a Sabon Bidiyo

Bello Turji Ya ba Najeriya Zabin Yaki ko Zaman Lafiya a Sabon Bidiyo

  • Babban dan ta'adda a Najeriya, Bello Turji ya fito a wani bidiyo yana cewa sun kai hare-hare kan jami'an tsaro a yankunan Sokoto da Zamfara
  • Ya ce mayakan shi na shirye domin tattaunawa da hukuma, amma kuma zai cigaba da fafatawa da jami'an tsaro idan aka zabi yaki da shi
  • Har yanzu jami'an tsaro ba su tabbatar da cewa ya kai hare-haren da ya fada a cikin bidiyon ba saboda ba su yi martanin maganganunsa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Wani bidiyo da ake zargin ya nuna fitaccen shugaban 'yan bindiga Bello Turji na yawo a kafafen sada zumunta, inda wanda ake nema ruwa a jallo ya yi ikirarin kai hare-hare.

Ya ce ya kai hare-hare ne a wasu sassan jihohin Sokoto da Zamfara, tare da bayyana cewa kungiyarsa a shirye take ta tattauna da gwamnati amma kuma tana cikin shirin yaki.

Kara karanta wannan

Shettima, gwamnoni, malamai, sarakuna sun hallara taron tuna mamar Tinubu

Kasurgumin dan ta'adda, Bello Turji
Babban dan ta'adda a Najeriya, Bello Turji. Hoto: Zagazola Makama
Source: UGC

A cikin bidiyon da aka a sanya ranar 20 ga Yuni, 2026, Punch ta wallafa cewa mutumin da ya rufe fuskarsa, wanda ake kyautata zaton Turji ne, ya bayyana tare da wasu dauke da makamai sanye da kayan sojoji.

'Ko sulhu ko yaki,' Turji

Jagoran 'yan bindigar ya yi amfani da bidiyon wajen magana kan yiwuwar sulhu da hukumomi, inda ya nuna aniyarsa ta shiga tattaunawa idan gwamnati ta zabi hanyar sasanci maimakon ta amfani da karfin soja.

A cewarsa:

"Idan gwamnati a shirye take domin tattaunawa, mu ma a shirye muke domin tattaunawa. Amma idan suna son ci gaba da amfani da karfi, mu ma mun shirya. Mayakanmu a shirye suke domin duk abin da zai zo."

Daily Trust ta wallafa cewa ya yi magana yana mai ikirarin cewa kungiyarsa ta dauki fansa kan wadanda ke kai masu hare-hare a Zamfara da Sokoto.

Ya kuma nuna cewa kungiyarsa ba za ta janye daga daukar makami ba, yana cewa:

Kara karanta wannan

An fallasa shirin shawo kan talaka da shinkafa da taliya a zaben gwamnan Ekiti

"A shirye muke domin zaman lafiya, amma idan suka zabi yaki, mu ma a shirye muke. Za mu kare kanmu."
Taswirar jihar Sokoto
Taswirar jihar Sokoto a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Duk da cewa kalaman Turji sun ja hankalin jama'a sosai a kafafen sada zumunta, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba game da abubuwan da ke cikin bidiyon.

Ga bidiyon da dan ta'adda Bello Turji ya yi magana da shafin GoldMyneTV ya wallafa a X:

Sojoji za su yi aiki da 'yan jarida

A wani labarin, mun kawo muku cewa ministan tsaro, Janar Christopher Musa ya bayyana cewa suna shirin sauya salon yaki da 'yan ta'adda.

A wani bayani da ya yi, ya sanar da cewa za su fara shiga wuraren yaki da 'yan bindiga a daji tare da 'yan jarida domin daukar rahoton kai tsaye.

Ministan tsaron ya bayyana haka ne yayin wani taro da aka yi a Abuja, inda ya ce ya kamata a samu alaka mai kyau tsakanin sojoji da 'yan jarida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng