Kasa Ta Rikice: Gwamnonin Arewa 19 da Sarakunan Gargajiya Sun Sa Labule a Kaduna

Kasa Ta Rikice: Gwamnonin Arewa 19 da Sarakunan Gargajiya Sun Sa Labule a Kaduna

  • Gwamnoni da sarakunan gargajiya daga jihohin Arewa 19 sun hallara a Kaduna domin tattaunawa kan matsalolin tsaro da halin kuncin tattalin arziki
  • Shugaban gwamnonin Arewa, Gwamna Inuwa Yahaya, ya bukaci hadin kai wajen dakile matsalolin tsaro da koma-baya a ci gaban dan Adam a Arewa
  • Ya nemi a duba dabarun tsaro, a farfado da kamfanin NNDC, a saka jari a ilimi da matasa, tare da bai wa sarakuna matsayi a kundin tsarin mulki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Yayin da yankin Arewa ke ci gaba da fuskantar matsaloli, gwamnoni da sarakuna sun yi ganawa a Kaduna.

Manyan yankin daga jihohin Arewa 19 sun hallara a gidan gwamnatin Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna domin tattaunawa kan matsalolin da suka shafi yankin.

Gwamnonin Arewa sun gana a Kaduna
Gwamnonin Arewa 19 sun yi zama a Kaduna. Hoto: Ismaila Uba Misilli.
Asali: Facebook

Gwamnonin Arewa da sarakuna sun gana a Kaduna

Sakataren yada labaran gidan gwamnatin jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli shi ya tabbatar da haka a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Misilli ya ce taron na matakin koli karkashin kungiyar Gwamnonin Arewa (NSGF) na gudana ne karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya.

A jawabin bude taro, Gwamna Inuwa ya bayyana matsalolin da ke addabar jihohin Arewa, yana mai nuna bukatar hadin gwiwa da gaggawar daukar mataki.

Ya ce:

“Ina matukar damuwa da yadda matsalar tsaro ta tsananta, muna Allah-wadai da kisan mutane a jihohin Plateau, Bauchi da sauransu."

Ya bukaci a sake nazarin tsare-tsaren tsaro tare da hada kai tsakanin matakan gwamnati domin dawo da zaman lafiya da kare rayukan jama’a.

Baya ga matsalar tsaro, Gwamna Inuwa ya bayyana damuwa kan yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da hauhawar talauci da raunana tattalin arziki.

Ya bukaci a farfado da kamfanin NNDC da kuma saka jari a fannin ilimi da horar da matasa domin fitar da yankin daga dogaro da taimako.

Gwamnonin Arewa sun gano matsalolin yankin
Gwamnonin Arewa 19 da Sarakuna sun gana a Kaduna. Hoto: Ismaila Uba Misilli.
Asali: Facebook

Gwamna Inuwa ya shiga damuwa kan Arewa

Inuwa ya bayyana damuwa kan yadda aka yi watsi da muhimman ayyukan ababen more rayuwa a Arewa, yana mai cewa hadin gwiwar masu ruwa da tsaki na da amfani.

Gwamnan ya ce ya kamata sarakunan gargajiya su samu matsayi a tsarin mulki domin taka rawar gani wajen warware rigingimu da zaman lafiya.

Ya kara cewa:

“Ya zama dole mu fice daga fifita muradun kai domin kawo sauyi. Arewa na kallo, kuma tarihi zai yi mana hukunci da aikace-aikacenmu."

Tattaunawa na ci gaba a sirrance, inda ake sa ran za a fitar da sanarwar taro a ƙarshe domin karin bayani kan batutuwa da aka magantu kansu yayin taron.

Manyan Arewa sun nemowa yankin mafita

A baya, mun ba ku labarin cewa Ƙungiyar ACF ta tunatar da gwamnatoci muhimmancin ɗaukar matakan kariya gabanin faruwar ambaliya yayin da ake tunkarar daminar bana.

Manyan Arewa sun buƙaci gwamnatin tarayya, da ta jihohi da ƙananan hukumomi su shirya domin daƙile illar ambaliya.

Kungiyar ACF ta kuma yi kira ga mazauna garuruwan da ake hasashen za a iya fuskantar ambaliya da su kare mahallansu da gujewa toshe hanyoyin ruwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.