Gwamnonin Arewa za Su Yi Taro na Musamman a Kaduna kan Matsalar Tsaro

Gwamnonin Arewa za Su Yi Taro na Musamman a Kaduna kan Matsalar Tsaro

  • Gwamnonin Arewa sun shirya ganawa a Kaduna don tattauna yadda za a dakile harin ta’addanci da ke kara kamari a yankin
  • Hakan na zuwa ne bayan hare-hare sun hallaka akalla mutane kimanin 133 a cikin kwanaki kadan a jihohin Arewa daban-daban
  • Baya ga hare hare, sabuwar kungiyar 'yan ta’adda mai suna Mahmuda ta bulla a jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiyan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Gwamnonin Arewa sun shirya wani muhimmin taro da za a gudanar a yau Asabar, 10 ga Mayu, 2025 a Kaduna.

Rahotanni sun bayyanna cewa za a yi taron ne domin duba yadda za a shawo kan matsanancin halin rashin tsaro da ke addabar yankin.

Gwamnoni
Gwamnonin Arewa za su yi taro a Kaduna kan tsaro. Hoto: Uba Sani
Asali: Twitter

Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa ne ya kira taron, kamar yadda daraktan yada labaran gidan gwamnatin Gombe, Ismaila Uba Misilli ya tabbatar wa da jaridar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Misilli ya ce an riga an amince da gudanar da taron, kuma batun tsaro ne a saman jadawalin tattaunawar da za a yi

Hare-hare sun jawo mutuwar mutanen Arewa

Rahoto ya nuna cewa a cikin makonni biyu da suka gabata, akalla mutane 133 ne suka mutu a sanadiyyar hare-hare daban-daban da suka faru a sassa daban-daban na Arewa.

Daga ranar 24 ga Afrilu zuwa 7 ga Mayu, hare-haren Boko Haram, ISWAP, Lakurawa, da kuma sabuwar kungiyar Mahmuda sun janyo asarar rayuka da dama da barnar dukiya.

A ranar 7 ga Mayu ne aka kashe wani Kyaftin din soji da wani jami'in soji a Izge, karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Mai martaba Sarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Shehu Timta ya tabbatar da aukuwar harin da kisan babban jami'in.

Hare-hare a jihohin Benue, Bauchi da Yobe

A daren Talata, 6 ga Mayu, wasu 'yan bindiga sun kai hari a yankin Gwer na jihar Benue inda suka kashe wani jigon APC, Akaabo Johnson da wasu mutane uku.

A ranar Lahadi, 4 ga Mayu, akalla mutane 25 sun mutu a Alkaleri, Bauchi yayin wata arangama tsakanin ‘yan sa kai da ‘yan bindiga.

Baya ga haka, an ruwaito cewa wasu mutane 19 da sun mutu a Gwana sakamakon harin masu satar shanu.

A Yobe kuwa, a ranar Juma’a, 2 ga Mayu, ‘yan kungiyar ISWAP sun kai hari sansanin sojoji inda suka kashe akalla sojoji 11, kamar yadda majiyoyi daga rundunar soji suka tabbatar.

Gwamnonin Arewa
Gwamnonin Arewa ta Yamma yayin wani taro kan tsaro. Hoto: Uba Sani
Asali: Facebook

Abin da gwamnonin Arewa za su tattauna

Rahotanni sun bayyana cewa taron gwamnonin Arewa zai nazarin sababbin dabarun yaki da ta’addanci.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Jigawa, Garba Muhammad ya wallafa a Facebook cewa gwamnonin Arewa ta Yamma sun yi taro a Kaduna a jiya Juma'a.

Ana sa ran taron zai haifar da sababbin matakai masu karfi da za su dakile hare-haren da ke hana jama’a zaman lafiya a sassan Arewa.

An kashe 'yar shekara 1 a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa wasu masu garkuwa sun sace yarinya 'yar shekara guda kuma sun kashe ta a jihar Kano.

Rahotanni sun tabbatar da cewa masu garkuwar sun kashe yarinyar kuma suka wurga gawarta wata rijiya.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yaba da kokarin hukumar DSS na cafke mutane 5 da ake zargi da hannu a lamarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng