Zargin Satar N528bn: Cece Kuce Ya Kaure tsakanin wasu 'Yan Arewa da Matawalle

Zargin Satar N528bn: Cece Kuce Ya Kaure tsakanin wasu 'Yan Arewa da Matawalle

  • Kungiyar Concerned Northern Forum zargi tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle da karkatar da Naira biliyan 528 lokacin da yake mulki
  • Kungiyar ta ce ana zargin ya karkatar da kudin ne daga asusun raba kudi na tarayya da na hadin gwiwa da ƙananan hukumomi (JAAC)
  • Shugaban kungiyar, Alhaji Aliyu Sani, ya bayyana cewa sun gabatar da takardun korafi zuwa Hukumar EFCC da ke yaki da cin hanci da rashawa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Cece -kuce ya barke tsakanin Kungiyar Arewa ta Concerned Northern Forum da Ministan Tsaro na Ƙasa, Bello Matawalle, kan zargin wawure kudin talakawa a Zamfara.

Kungiyar ta zargi Dr. Bello Matawalle da wawure Naira biliyan 528 a lokacin da yake gwamnan Jihar Zamfara daga shekarar 2019 zuwa 2023.

Matawalle
Wata kungiyar Arewa ta zargi Matawalle da satar kudin jama'a Hoto: Dr. Bello Matawalle
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa shugaban kungiyar, Alhaji Aliyu Sani, ne ya jagoranci taron manema labarai a Kaduna a ranar Litinin, inda suka caccaki tsohon gwamnan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar Arewa ta caccaki Bello Matawalle

Premium Times ta ruwaito cewa an zargi Matawalle da wawashe kudi daga Asusun Raba Kudin Tarayya (FAAC), Asusun Hadin Gwiwar Jiha da Ƙananan Hukumomi (JAAC), da bashin cikin gida.

Shugaban kungiyar, Aliyu Sani, ya bayyana takaicinsa bisa rashin daukar mataki daga Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), duk da cewa sun gabatar da korafe-korafe a hukumance.

Ya ce:

“Mun tattara hujjoji da bayanai dangane da zargin wawure makudan kudi da aka yi a jagorancin Bello Matawalle."
"Wadannan ba zarge-zarge marasa tushe ba ne. Mun yi tsammanin bincike zai ci gaba bayan ziyararmu ta baya ga hedikwatar EFCC, amma har yanzu babu wani cigaba.”
Matawalle
An musanta cewa Bello Matawalle ya saci kudin mutanen Zamfara Hoto: Dr. Bello Matawalle
Asali: Facebook

Ya jaddada cewa dole ne Matawalle ya fayyace yadda aka kashe kudin FAAC har N290bn, da na JAAC N133bn, da bashin da aka karbo na N105bn da aka samu a lokacin gwamnatinsa.

Makusancin Matawalle ya soki kungiyar Arewa

Tsohon mai ba Bello Matawalle shawara na musamman, Suleiman Shuaibu, ya kare ubangidansa, inda ya zargi kungiyar da nuna hassada saboda ci gabansu a siyasa.

Ya ce:

“Na san yadda kasafin kudin jihar yake. Na san yadda kudin FAAC ke zuwa, kuma na san yadda aka raba su. Na san abinda muka bari a baitul-mali na jihar Zamfara – Naira biliyan 11 kafin mika mulki.”

Suleiman Shuaibu ya ce yana cikin kwamitin mika mulki da aka kafa daga bangarorin gwamnati mai barin gado da sabuwar gwamnati, domin tabbatar da mika mulki lafiya.

Kwamishinan Matawalle ya soki gwamnan Zamfara

A baya, mun wallafa cewa tsohon kwamishinan yaɗa labarai na jihar Zamfara a ƙarƙashin gwamnatin Bello Matawalle, Ibrahim Dosara, ya caccaki Gwamna Dauda Lawal.

Dosara ya yi wannan martani ne yayin da yake tsokaci a kan wata ganawa da Gwamnan Zamfara mai ci, Dauda Lawal ya yi da manema labarai, ya ce N4m kawai ya gada.

Dosara ya bayyana furucin Gwamnan a matsayin karya tsagwaronta wacce ba ta da tushe kuma bai kamata jama’a su yarda da ita ba, ganin cewa Matawalle bai wawuri kudin talakawa ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.