NWDC Ta Soke Tallafin Karatu, An Fasa Tura 'Yan Arewa zuwa Kasashen Waje
- Hukumar NWDC ta sanar da soke shirin tallafin karatun waje bisa umarnin gwamnatin tarayya na mayar da hankali kan ilimi a cikin gida
- Bayan hukumar raya Arewa maso Yamma ta sanar da fara fitar da dalibai waje domin karo karatu, sai gwamnati ta ba da umarnin soke matakin
- NWDC ta ce za ta fitar da bayani kan sababbin shirye-shiryen ci gaba da suka dace da manufofin gwamnatin tarayya da za su taimakawa yankin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Hukumar bunkasa Arewa maso Yamma (NWDC) ta sanar da soke sabon shirin tallafin karatu na kasashen waje da ta bayyana a baya-bayan nan.
Ta sanar da cewa ta dauki wannan matakin ne bisa sabon umarnin da ta samu daga gwamnatin tarayya domin mayar da hankali kan ci gaban ilimi a cikin gida.

Asali: Facebook
A wani sako da hukumar NWDC wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa matakin ya yi daidai da kudirin gwamnatin tarayya na karfafa cibiyoyin ilimi na cikin gida da habaka su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NWDC ta bi umarnin gwamnatin tarayya
Leadership News ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta fiyar da sanarwar ne a kokarinta na inganta cibiyoyin cikin gida da karfafa yadda ake ilimatar da jama'a.
Wani bangare na sanarwar ya ce:
“Hukumar bunkasa Arewa maso Yamma (NWDC) na sanar da soke tsarin karatun kasashen waje, bisa umarnin gwamnatin tarayya na baya-bayan nan da ke bukatar mayar da hankali kan ilimi a cikin gida a Najeriya.”
Kafin nan Daily Trust ta rahoto yadda aka samu sabani a hukumar a game da tsarin.
Ana zargin akwai sabani tsakanin shugabannin NWDC da majalisar da ke sa ido game da aikin hukumar raya yankin na Arewa ya Yamma.
Wane mataki NWDC ta dauka na gaba?
A halin yanzu, hukumar NWDC ba ta bayyana wani madadin tallafin karatu ba bayan soke shirin na kasashen waje.

Asali: Twitter
Sai dai hukumar ta tabbatar da cewa za ta sanar da al'umma a kan sababbin shirye-shiryen ci gaba na yankin da zarar an kammala tsarawa.
A cewar sanarwar:
“Hukumar na nan daram wajen daidaita shirye-shiryenta da manufofin da gwamnatin tarayya ta gindaya."
A ranar 7 ga Mayu, 2025, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta sanar da soke shirin tallafin karatu na waje, inda ta jaddada cewa gwamnatin tarayya na kokarin inganta tsarin ilimi a cikin gida.
Mrs. Folasade Boriowo, daraktar yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, ce ta fitar da sanarwar inda ta ce gwamnati za ta fi karkata hankali wajen daukar matakai ci gaban Najeriya.
NWDC za ta warware matsalolin Arewa
A wani labarin, mun wallafa cewa Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya bayyana cewa hukumar raya yankin Arewa maso Yamma za ta kawo sauki ga jama'a.
Ya ce hukumar NWDC za ta taimaka wajen magance matsalolin da ke damun jihohin Arewa maso Yamma guda bakwai, wato: Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Jigawa, Sokoto da Zamfara.
Barau ya jaddada cewa hukumar NWDC za ta taka muhimmiyar rawa wajen farfado da yankin ta hanyar warware matsalolin tsaro, bunkasa aikin noma, da gina ababen more rayuwa a shiyyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng