Gwamna Zulum Ya Yi Tone Tone, Ya Zargi Wasu Ƴan Siyasa da Sojoji da Taimaka Wa Boko Haram
- Gwamna Babagana Umaru Zulum na jihar Borno ya yi zargin cewa wasu ƴan siyasa da sojoji na taimaka wa ƴan Boko Haram
- Zulum ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta kara inganta ayyukan leken asiri tare da hukunta duk wanda aka gano yana cin amanar ƙasa
- Ya kuma koka kan rashin kayan aiki na zamani da sojoji ke fama da shi, yana mai cewa ƴan ta'adda sun koma amfani da fasahar zamani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Borno - Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya zargi wasu ‘yan siyasa da jami’an rundunar soji da bai wa ƴan ta'addan Boko Haram bayanan sirri da haɗe kai da su.
Gwamna Zulum ya yi zargin cewa akwai imfomomi a cikin ƴan siyasa da sojoji, waɗanda ke taimakawa ƴan ta'addan Boko Haram wajen aikata mugayen laifuka a Borno.

Asali: Twitter
Babagana Zulum ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a ranar Laraba, 21 ga watan Mayu, 2025, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zulum ya faɗi masu taimakon Boko Haram
Ya ce gwamnatin jihar Borno za ta karfafa hanyoyin leken asiri da kuma hukunta masu cin amanar kasa ba tare da sassauta masu ba, kamar aka kawo.
“Muna da imfomomi a cikin sojoji, ƴan siyasa da ma al'umma, waɗanda ke taimakon ƴan ta'adda kuma su haɗa kai da su.
"Abin da za mu yi shi ne, mu karfafa leken asiri da kuma hukunta su ba tare da sassauci ba. Mu cire siyasa a lamarin nan, cikin watanni shida za mu iya kawo karshen matsalar.”
- Farfesa Zulum.
Wani hali ƴan ta'addan da suka mika wuya ke ciki?
Game da batun wadanda suka mika wuya daga cikin ‘yan ta’adda, Gwamna Zulum ya ce ba duka suka gyara halayensu ba, amma yawancinsu suna bada gudunmawa mai kyau.
A rahoton Daily Trust. Zulum ya ce:
“Ba zan ce kashi 100 na wadanda suka mika wuya sun shiryu ba, amma ina tabbatar da cewa sama da kashi 99 na su suna bin doka kuma ba sa da hannu ayyukan ta’addanci.”
Hanyoyin da za a bi don magance ta'addanci
Zulum ya nanata cewa ya zama dole Najeriya ta hada dabarun soja, hanyoyin inganta zamantakewa da tattalin arziki domin yaki da ta’addanci.
"Ƙarfin soji kaɗai ba zai magance ta'addanci ba, dole mu biyo sauran matakai da suka kamata domin dawo da zsman lafiya," in ji shi.
Ya kara da cewa rundunar soji ba ta da kayan aiki da suka dace don yaki da ta’addanci, yayin da ‘yan ta’addan ke amfani da fasahar zamani wacce ta fi ta jami'an tsaronmu.

Asali: Facebook
Sai dai duk da haka, Farfesa Zulum ya yabawa rundunar sojin Najeriya bisa gudunmawar da take bayarwa wajen samar da zaman lafiya ta kowane fanni.
Ya roki Shugaba Bola Tinubu da ya saurari shawarwari daga kwararru da kuma mutanen da suka fahimci gaskiya game da wannan matsala ta tsaro.
Boko Haram ta kashe mutane 90 a Borno
A wani labarin, kun ji cewa ƴan ta'addan Boko Haram/ISWAP sun kashe manoma da masunta akalla 90 a hare-hare daban-daban a jihar Borno.
An tattaro cewa ƴan ta'addan suk aikata wannan ɗanyen aiki ne a cikin watanni biyar a yankin Tafkin Chadi da ke cikin jihar Borno a Arewa maso Gabas.
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta bayyana damuwa kan yadda mayakan Boko Haram ke ci gaba da kashe jama’a ba tare da an taka masu birki ba.
Asali: Legit.ng