Tafiyar El Rufa'i Ta Yi wa APC Lahani a Gombe, Sama da Mutum 2,000 Sun Koma SDP

Tafiyar El Rufa'i Ta Yi wa APC Lahani a Gombe, Sama da Mutum 2,000 Sun Koma SDP

  • Fiye da mambobi 2,000 daga APC da PDP sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar SDP yayin bikin buɗe ofishin jam’iyyar a Dukku
  • Shugaban jam’iyyar na jiha, Adamu Modibbo, ya ce wannan al’amari wata alama ce ta farin jinin SDP a tsakanin matasa da jama’ar karkara
  • An yi addu’o’in zaman lafiya da nasara ga jam’iyyar yayin da mutanen SDP suka bayyana burinsu na yin mulkin gaskiya a 2027

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Jam’iyyar SDP ta sake girgiza siyasar Jihar Gombe, bayan da mambobi sama da 2,000 daga manyan jam’iyyu biyu na APC da PDP suka sauya sheƙa zuwa SDP.

Mutanen sun sauya shekar ne a wani babban taron siyasa da aka gudanar a ƙaramar hukumar Dukku.

SDP Gombe
SDP ta karbi mutane sama da 2,000 a Gombe. Hoto: Shehu Musa Gabam
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda taron ya gudana ne a cikin wani sako da shugaban SDP na kasa, Shehu Musa Gabam ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron ya ya wakana ne yayin bikin buɗe sabon ofishin SDP na ƙaramar hukumar Dukku wanda shugaban jam’iyyar na jiha, Kwamared Adamu Abubakar Modibbo, ya jagoranta.

Yawan waɗanda suka sauya sheƙar, da galibinsu matasa ne ya nuna yadda jam’iyyar SDP ke ƙara samun karɓuwa a lungu da sako na jihar.

Burin jam'iyyar SDP a jihar Gombe

A jawabinsa yayin bikin, Kwamared Modibbo ya nuna gamsuwa da yadda mutane suka halarci taron.

Shugaban jam'iyyar ya bayyana cewa SDP za ta ci gaba da ba wa jama’a damar fitowa fili su faɗi ra’ayinsu da neman ci gaban yankinsu.

Ya ce:

“Wannan rana ce ta tarihi a Dukku. Mun buɗe sabon babi a harkar siyasa. In sha Allah, za mu dawo nan a 2027 domin murnar nasarar talakawa ta hannun SDP.”

Ya ƙara da cewa jam’iyyar za ta maida hankali kan samar da ruwa, hanyoyi da kuma tallafawa noma domin sauƙaƙa rayuwa ga jama’ar Dukku.

SDP Gombe
Wasu 'yan SDP da suka sauya sheka a Gombe a kwanakin baya. Hoto: Shehu Musa Gabam
Asali: Facebook

Jawabin shugaban jam'iyyar SDP a Dukku

A nasa jawabin wakilin jam’iyyar SDP a Dukku, Alhaji Ali Muhammad Ajasco ya tabbatar wa shugabannin jam’iyyar da cewa za su ci gaba da jajircewa wajen jawo mambobi.

Ya ce jama’a sun gaji da irin salon siyasar da suka saba gani daga manyan jam’iyyu, kuma sun yanke shawarar ba wa SDP dama domin samun sabuwar rayuwa mai kyau.

An rufe taron SDP da addu’a a Gombe

An kammala taron da addu’o’i na musamman domin neman nasara, haɗin kai da zaman lafiya ga jam’iyyar SDP.

Haka kuma, an roƙi Allah ya tsare duk waɗanda suka halarci taron a hanyarsu ta komawa gidajensu.

Matan NNPP a Kano sun sauya sheka

A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karbi wasu matan NNPP zuwa APC.

Matan sun bayyana cewa rikicin jam'iyyar NNPP ne ya tilasta musu sauya shekar domin samun cigaba.

Sanata Barau Jibrin ya yi maraba da matan, yana cewa sun dauki matakin da ya dace tare da yin alkawarin tafiya tare da su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng