2027: An Fitar da Tsarin Nasarar Tinubu a Arewa da Miliyoyin Kuri'un da zai Samu

2027: An Fitar da Tsarin Nasarar Tinubu a Arewa da Miliyoyin Kuri'un da zai Samu

  • Wata kungiyar matasa daga jihohin Arewa 19 da Abuja ta kai wa Sanata Barau Jibrin ziyara tare da mika masa tsarin samun nasarar APC a 2027
  • Shugaban kungiyar, Kwamared Auwal Ibrahim Sansani, ya bayyana cewa za su iya samar wa Shugaba Bola Tinubu kuri’u 5,591,468 a yankin Arewa
  • Sanata Barau ya yaba da shirin matasan, yana mai cewa nasara tana farawa ne da ingantaccen tsari da hadin kai daga kungiyoyi daban-daban

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Yayin da shirin siyasar 2027 ke kara daukar zafi a Najeriya, kungiyoyi daban-daban na ci gaba da bayyana goyon bayansu ga shugabanni.

Wata kungiyar magoya bayan Tinubu a Arewa (TNYF) ta ziyarci Sanata Barau Jibrin domin mika masa wata takarda mai dauke da shirin nasarar Shugaba Bola Tinubu.

Tinubu
An yi wa Bola Tinubu alkawarin kuri'u miliyan 5 a Arewacin Najeriya
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan ziyarar ne a cikin wani sako da mataimakin shugaban majalisar dattawan ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasa za su kawo kuri’u miliyan 5 ga Tinubu

Shugaban kungiyar, Kwamared Auwal Ibrahim Sansani, ya bayyana cewa kungiyar matasan ta tsara yadda za ta iya samar wa Shugaba Tinubu kuri’u miliyan 5.5 a yankin Arewa.

Ibrahim Sansani ya ce tsarin yana dauke da matakai na musamman da za su shafi aikin wayar da kai da kuma hadin gwiwa da shugabannin al’umma da na siyasa.

Shugaban sashen bincike da ICT na kungiyar, Adamu Ahmed Suleiman, ya ce sun gudanar da bincike da tattara bayanai a fadin Arewa domin tabbatar da yiwuwar nasarar shirin.

Sanata Barau ya yaba wa matasan Arewa

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya nuna jin dadinsa kan yadda matasan suka fitar da gagarumin tsarin.

Sanata Barau ya ce:

“Idan har wannan kungiya kadai za ta iya samar da kuri’u kusan miliyan 6, to muna da tabbacin samun nasara mai rinjaye in sha Allah.”

Ya kuma jaddada cewa Shugaba Tinubu yana da niyyar gaske wajen gyara Najeriya, don haka ya bukaci kowa da kowa da ya ba shi goyon baya.

Tinubu
An yi wa Bola Tinubu alkawarin kuri'u miliyan 5 a Arewacin Najeriya
Asali: Facebook

Barau ya bukaci marawa Tinubu baya a 2027

Sanata Barau Jibrin ya kara da cewa yana da muhimmanci ‘yan Najeriya su goyi bayan shugabansu, musamman ganin cewa ranar 29 ga Mayu zai cika shekaru biyu da fara mulkinsa.

Ya ce shirye-shiryen shugaba Bola Tinubu na bukatar hadin gwiwar kowa domin ciyar da Najeriya gaba da tabbatar da cigaba mai dorewa.

Barau ya karbi 'yan NNPP zuwa APC

A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa ya karbi wasu mata 'yan jam'iyyar NNPP da suka hakura da tafiyar Kwankwasiyya a jihar Kano.

Matan sun fito daga yankunan Kano inda suka ce sun gaji da yadda rikicin gida ya dabaibaye jam'iyyar NNPP a jihar Kano da Najeriya.

Bayan karbar matan zuwa jam'iyyar APC, Sanata Barau Jibrin ya musu alkawarin cewa za a tafi da su tare ba tare da nuna bambanci ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng