'Abin da Ƴan Arewa maso Yamma Za Su Yi wa Tinubu da Gwamnoni 5 kafin Zaben 2027'

'Abin da Ƴan Arewa maso Yamma Za Su Yi wa Tinubu da Gwamnoni 5 kafin Zaben 2027'

  • Hakeem Baba-Ahmed ya ce ƴan Arewa maso Yamma za su yi wa ƴan siyasa alkalanci daidai da halin da suka jefa su a ciki
  • Tsohon hadimin mataimakin shugaban ƙasa ya ce ƴan yankin za su duba talauci, tashin hankali da ƙuncin da suke ciki wajen kaɗa kuri'a a zaɓen 2027
  • Hakeem ya yi wannan magana ne a matsayin martani ga matakin masu ruwa da tsakin APC da suka goyi bayan tazarcen Bola Tinubu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Tsohon mai bai wa mataimakin shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce jama'ar Arewa maso Yamma za su yi wa ƴan siyasa alkalanci a 2027.

Hakeem ya bayyana cewa ƴan yankin za su ɗora shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da sauran shugabanninsu a sikeli kafin su yanke hukunci a zaɓe na gaba.

Hakeem Baba-Ahmed.
Hakeem Baba-Ahmed ya ce da alama ƴan APC sun manta da jama'ar da za su masu alƙalanci a 2027 Hoto: Hakeem Baba Ahmed
Asali: Twitter

Tsohon hadimin Kashim Shettima ya bayyana haka ne da yake martani kan matsayar da masu ruwa da tsakin APC suka cimma a taron da suka yi a Kaduna, inji rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane abu ƴan Arewa maso Yamma za su yi?

Ya ce mutanen yankin Arewa maso Yamma za su yi wa 'yan siyasa alkalanci bisa wahalhalun da suka sha na tashin hankali, kashe-kashe da talauci a zaben 2027.

Hakeem Baba-Ahmed, wanda kwanan nan ya yi murabus daga gwamnatin Tinubu, ya bayyana cewa gwamnoni a yankin suna gudanar da mulki tamkar ba su damu da halin da jama’a ke ciki ba.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan goyon bayan da jam’iyyar APC ta Arewa maso Yamma ta bai wa Shugaba Tinubu.

Masu ruwa da tsakin APC sun goyi bayan Tinubu

Masu ruwa da tsakin APC a yankin sun jaddada goyon bayansu ga Bola Tinubi domin ya yi tazarce a zabe 2027.

A taron da suka yi a Kaduna, Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Tajudeen Abbas, ne ya gabatar da kudurin goyon bayan Tinubu, wanda Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya mara wa baya.

Sannan masu ruwa da tsakin APC suka kada kuri’ar amincewa da tazarcen Shugaban Ƙasa Tinubu a zaɓen 2027.

An kuma sanar da cewa gwamnonin APC biyar na yankin Arewa maso Yamma za su samu tikitin tsayawa takara kai tsaye a 2027 ba tare da hamayya ba.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje ne ya bayyana hakan, yana mai cewa Shugaba Tinubu ya himmatu wajen ci gaban yankin da kasa baki daya.

Hakeem Baba Ahmed.
Hakeem Baba Ahmed ya ce ƴan Arewa maso Yamma za su sa shugabanni a sikeli kafin zaɓen 2027 Hoto: @ImranMuhdz
Asali: Twitter

Hakeem Baba-Ahmed ya yi martani

Amma da yake martani, Hakeem Baba-Ahmed ya ce:

"Gwamnonin APC na Arewa maso Yamma sun goyi bayan Tinubu, sun goyi bayan kansu, da dukan zaɓaɓɓu da waɗanda suka sauya sheka a yankin.
"Sun manta da jama’a, waɗanda za su yi musu alkalanci bisa abubuwan da suka fuskanta na tashin hankali, kashe-kashe da talauci. Ga dukkan alamu suna ganin duk wannan ba komai ba ne."

Tanko Yakasai ya yi hasashen 2027

A wani labarin, kun ji cewa ɗaya daga cikin manyan kungiyar ACF ta manyan Arewa, Tanko Yakasai ya ce ba mai iya ja da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Ya ce jam'iyyar APC mai mulki ita ke da iko da mafi yawan jihohin ƙasar nan kuma tana ci gaba da samun goyon baya daga gwamnonin tsagin adawa.

Tanko Yakasai ya ce a halin yanzu, babu wani ɗan siyasa da ke da goyon baya mai ƙarfi wanda zai iya ja da Tinubu a faɗin ƙasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262