Kungiyar Arewa Ta Nuna Gwamnan Zamfara da Yatsa, Tana So Ya Yi Murabus nan Take

Kungiyar Arewa Ta Nuna Gwamnan Zamfara da Yatsa, Tana So Ya Yi Murabus nan Take

  • Wata kungiya a Arewa maso Yamma ta buƙaci Gwamna Dauda Lawal ya yi murabus saboda gazawarsa wajen magance matsalar tsaro
  • COGGAN ta ce Dauda ya kasa cika alkawuran da ya dauka, ciki har da na kawo ƙarshen 'yan bindiga cikin watanni uku kacal a jihar Zamfara
  • Ƙungiyar ta bukaci a gwamnan ya bayyana yadda yake kashe kuɗaɗen Zamfarawa, tana mai cewa jihar ta cancanci shugabanci nagari

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Ƙungiyar farar hula da ke rajin samar da shugabanci nagari da bin diddigin ayyukan gwamnati a Arewa maso Yamma (COGGAN) ta nemi Gwamna Dauda Lawal ya yi murabus.

Ƙungiyar COGGAN ta buƙaci gwamnan na Zamfara da ya sauka daga mulki saboda gazawar gwamnatin sa na magance matsalar tsaro da kuma inganta ilimi.

An taso Dauda Lawal a gaba, ana so ya yi murabus daga gwamnan Zamfara
Mai girma gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal. Hoto: @daudalawal_/X
Asali: Facebook

An zargi gwamnan Zamfara da gaza cika alkawari

Kungiyar ta bayyana wannan matsayar ne a cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Alhaji Ibrahim Anka, ya sa wa hannu a ranar Talata, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Ibrahim Anka ya bayyana cewa gwamnatin Dauda Lawal ta kasa cika alkawuran da ta daukar wa jama’a tun bayan da ta hau mulki a 2023.

Ya tuna cewa Gwamna Dauda Lawal da kansa ya sha alwashin kawo ƙarshen 'yan bindiga cikin watanni uku a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023.

Amma a cewarsa, sun yi mamakin yadda ya shafe fiye da shekara guda ba tare da cika alkawarin ba, illa ma matsalar tsaro da ta cigaba da ta’azzara a sassan jihar.

Bayan tsaro, an fito da wata matsalar Zamfara

Ƙungiyar COGGAN ta nuna damuwa kan yadda hare-haren 'yan bindiga ke cigaba da addabar al’umma, tare da lalata harkokin noma, kasuwanni na karkara da kuma tsarin ilimi a jihar.

Sanarwar ta bayyana cewa halin da ake ciki ya sa mutane da dama cikin fargaba tare da hana su gudanar da rayuwarsu yadda ya kamata.

A fannin ilimi, ƙungiyar ta jaddada cewa babu gagarumin cigaba da aka samu, inda ta ce har yanzu Zamfara na fama da ƙarancin samun ingantaccen ilimi.

Alhaji Ibrahim Anka ya nuna damuwa da cewa gwamnatin jihar ta bar makarantu ba tare da kayan more rayuwa a ba, kamar littattafai, tebura da kujeru, ko alluna na zamani.

Kungiyar Arewa ta ce gwamnan Zamfara ya gaza cika alkawuran da ya dauka, don haka ya yi murabus
Mai girma gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal. Hoto: @daudalawal_/X
Asali: Facebook

An nemi gwamnan Zamfara ya yi murabus

Kungiyar COGGAN ta kuma bukaci gwamnatin Dauda Lawal da ta dinga bayyana gaskiya da rikon amana wajen amfani da kuɗaɗen jama’a.

A cewar kungiyar, akwai bukatar gwamnati ta rika fadawa mutane yadda aka tafiyar da tallafin da gwamnatin tarayya ta bayar, musamman fadin yadda ake kashe su.

A ƙarshe, ƙungiyar ta buƙaci Gwamna Dauda da ya sauka daga kujerarsa, tana mai cewa mutanen Zamfara sun cancanci shugabanci nagari wanda zai fi mayar da hankali kan tsaro, ilimi da walwalar al’umma.

'Ka yi murabus' Hadimin Matawalle ga Dauda

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hadimin tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, Abdullahi Kaura, ya caccaki Gwamna Dauda Lawal kan tabarbarewar tsaro a jihar.

Kwamared Abduulahi Kaura ya bayyana cewa lokaci ya yi da Gwamna Dauda ya kamata ya sauka daga kan kujerarsa tun da ya gaza magance matsalar tsaro.

A cewarsa, tun da Gwamna Dauda Lawal ya hau mulki ne hare-haren ’yan bindiga da sace mutane suka kara ta’azzara a sassa da dama na jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.