'Ana Zuba Son Rai,' Naja'atu Mohammed Ta Zargi Tinubu da Mulkin Kabilanci
- Fitacciyar ‘yar siyasa, Naja’atu Mohammed, zargi Bola Tinubu da amfani da dukiyar ƙasa wajen bunƙasa yankinsa na Kudu maso Yamma
- Naja’atu ta caccaki gwamnati mai ci da cewa tsarin mukamai da ayyukan ci gaba sun fi karkata ga Yarbawa, abin da ke barazana ga kasa
- Ta bayyana cewa manufofin Tinubu sun jawo matsala ga rayuwar talakawa, inda ta ce mutane na fama da tsadar rayuwa a gwamnati mai-ci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Fitacciyar ‘yar siyasa, Hajiya Naja’atu Mohammed, ta bayyana damuwarta kan yadda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke tafiyar da mulkin kasar nan.
Hajiya Naja'atu, wacce sananniyar yar gwagwarmaya ce ta zargi shugaban kasan da nuna wariya da fifita yankinsa fiye da sauran shiyyoyin Najeriya.

Asali: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa, Naja’atu ta bayyana cewa manufofin Tinubu da tsare-tsarensa sun fi karkata ga yankin Yarbawa, musamman jihohin Kudu maso Yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Naja’atu ta caccaki salon mulkin Tinubu
Shugabar kungiyar Northern Star, ta ce tsarin mulkin Tinubu na son kai na amfani dukiyar ƙasa wajen bunƙasa yankinsa, maimakon a yi adalci daidai da tsarin mulkin tarayya.
Ta ce:
“Ba na da wata matsala da Tinubu a kashin kai, amma a fili yake cewa komai cikin gwamnatinsa na Yarbawa ne, kuma an yi saboda Yarbawa, kuma ta hanyar Yarbawa.”
Ta jaddada cewa ayyukan ci gaba na tarayya da mukaman gwamnati na da muhimmanci, amma an karkatar da yawansu zuwa yankin Kudu maso Yamma.
Ta kara da cewa:
“Tinubu na amfani da dukiyar ƙasa wajen gina yankinsa.”
Naja’atu ta caccaki manufofin gwamnatin Tinubu
Hajiya Naja’atu Mohammed ta bayyana rashin jin daɗinta game da yadda manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu ke shafar rayuwar talakawa.
Ta bayyana cewa tsare-tsaren da ya bijiro da su sun jawo hauhawar farashi da koma bayan tattalin arzikin jama'a.

Asali: Facebook
Ta ce:
“Ta yaya ƙasa za ta ci gaba da rayuwa idan manufofin gwamnati na karyar da ’yan ƙasa?”
Ta yi nuni da cewa irin waɗannan tsare-tsaren masu tsauri ba sa zuwa da wani tsarin tallafi ko sauƙin rayuwa ga talakawa.
Naja’atu ta jaddada cewa Najeriya na buƙatar gwamnati mai sauraron ra’ayin jama’a da gaggauta daukar matakan da za su rage wa talakawa wahala, ba wai kakaba manufofi ba tare da tuntuba ba.
Naja'atu ta zargi gwamnatin Tinubu da karfa-karfa
A baya, mun wallafa cewa fitacciyar ’yar gwagwarmaya a siyasar Arewacin Najeriya, Naja’atu Mohammed, ta bayyana damuwarta kan yadda gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke mulki.
Ta ce akwai yiwuwar a fara amfani da dokar ta-baci da barazana don murkushe ’yan adawa da wadanda jama'a suka zaba, kamar yadda aka yi a jihar Ribas na dakatar da gwamna.
Naja’atu ta ce jihar Kano na daya daga cikin jihohin da ake harara, tana zargin cewa akwai yunkuri daga bangaren gwamnatin tarayya na kakaba dokar ta-baci a jihar.
Asali: Legit.ng