Bayan Gargadin ’Yan Arewa a 2023, Naja’atu Ta Sake Bankado Wani Halin Tinubu

Bayan Gargadin ’Yan Arewa a 2023, Naja’atu Ta Sake Bankado Wani Halin Tinubu

  • Yar gwagwarmaya, Hajiya Naja’atu Mohammed ta caccaki shugabancin Bola Tinubu da laifin nuna wariyar yanki da gazawa a shugabanci
  • Ta bayyana cewa Tinubu yana fifita yankin Yarabawa da amfani da albarkatun kasa wajen ciyar da yankinsa gaba
  • Ta bukaci gyara da tattaunawa domin ceto Najeriya daga rugujewar dimokuradiyya da tattalin arziki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Yar gwagwarmaya, Hajiya Nàja’atu Mohammed ta sake yin magana kan salon mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Shugaba a kungiyar 'Northern Star', ta bayyana rashin jin dadinta game da salon shugabancin Tinubu a halin yanzu.

Naja'atu ta sake dura kan gwamnatin Tinubu
Naja'atu Mohammed ta caccaki salon mulkin Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Naja'atu ta zargi Tinubu da kabilanci a Najeriya

Hajiya Naja'atu ta bayyana haka ne a wata hirar farko na shirin 'Political Advantage Platform' na Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Naja'atu ta ce ba don wata husuma ba take sukar Tinubu, sai don kishin kasa da neman adalci ga kowa.

Ta zargi shugaban kasa Tinubu da nuna wariyar yanki, inda take cewa yana fifita Yarabawa kawai.

Nàja’atu ta bayyana cewa yawancin ayyukan gwamnati da manyan mukamai ana mayar da su zuwa yankin Kudu maso Yamma, musamman jihar Lagos.

Naja'atu ta zargi Tinubu da fifita Lagos

Ta bayar da misali da yadda ofisoshin gwamnati ke komawa Lagos daga Abuja, tana cewa hakan yana haifar da rabuwar kai a kasa.

Naja’atu ta ce irin wannan dabarar tana tattare da barazana ga hadin kan kasa da cigaba mai dorewa.

A bangaren tattalin arziki, ta suki cire tallafin man fetur, tana cewa an yanke wannan hukuncin ne ba tare da tuntubar 'yan Najeriya ba.

Ta bayyana cewa wannan mataki da sauran matakai sun jefa jama’a cikin talauci da wahala mai tsanani.

Naja'atu ta caccaki gwamnatin Tinubu
Naja'atu ta soki tsarin tattalin arzikin Tinubu. Hoto: Naja'atu Mohammed.
Asali: Twitter

Naja'atu ta magantu kan cire tallafin mai

Ta ce matakin cire tallafin fetur don biyan bukatun IMF ne, ba na ‘yan kasa ba inda ta ce farashin kaya ya hauyi mummunan tashi sama sosai kuma rayuwar mutane ta tabarbare.

Ta kara da cewa akwai bukatar gwamnati ta saurari kukan jama'a maimakon kawai bin shawarar kasashen waje.

Ta ce mutane na shan wahala sosai, kuma hakan zai iya haddasa rikicewar kasa.

A karshe, Naja’atu ta bukaci a dakatar da irin wannan mulki da ke kawo rarrabuwar kawuna inda ta nemi tattaunawa da gyare-gyare na gaggawa don ceto Najeriya.

Ta jaddada cewa dole ne a samar da shugabanci nagari wanda zai wakilci kowa, a cewarta, Najeriya na bukatar shugaba mai hangen nesa da adalci.

Naja'atu ta soki kama Farfesa Usman

A baya, kun ji cewa yar gwagwarmaya a Najeriya, Naja'atu Mohammed ta nuna ɓacin ranta kan tsarewa da kama Farfesa Usman Yusuf da aka yi a Abuja.

Yar gwagwarmayar ta yi ikirarin cewa gwamnatin Bola Tinubu ta kama tsohon shugaban NHIS ne domin ta rufe bakin masu faɗa maya gaskiya.

Naja'atu ta kasance mai sukar salon mulkin Bola Tinubu duba da halin da matakan gwamnatin suka rikita al'umma tun bayan hawansa mulkin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.