'Babu Yan Siyasa Masu Kwari,' Tanko Yakasai Ya ce Babu Mai Iya Tunkarar Tinubu a 2027
- Guda daga cikin wadanda suka kafa kungiyar ACF, Tanko Yakasai ya ce dukkanin alamu sun nuna Bola Tinubu zai koma ofis idan ya yi takara
- Ya bayyana cewa zuwa yanzu, babu wasu yan siyasa da ke da kwari ko farin jinin Tinubu a tsakanin yan siyasa da za su iya takara a 2027
- Yakasai ya ce matsalolin cikin gida a jam’iyyun adawa na kara sauƙaƙa wa Tinubu hanyar sake nasara a zaɓen da ke kara tunkarowa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Alhaji Tanko Yakasai, ɗaya daga cikin wadanda suka kafa ACF, ya ce shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ke da mafi rinjaye da kuma damar nasara a zaɓen shugaban ƙasa a 2027.
A cewarsa, jam’iyyar da ke mulki ta APC na da iko da mafi yawan jihohin ƙasar, kuma tana ci gaba da samun goyon bayan wasu gwamnoni daga jam’iyyun adawa.

Asali: Facebook
The Cable ta ruwaito cewa Yakasai ya ce a halin yanzu, babu wani ɗan siyasa da ke da goyon baya mai ƙarfi kamar Tinubu a faɗin ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tanko Yakasai game da Bola Tinubu
Vanguard News ta wallafa cewa, Tanko Yakasai ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na da cikakken goyon bayan gwamnoni da sauran manyan shugabanni a ƙasar.
Ya ce:
“A Najeriya a yau, Bola Tinubu ne shugaban ƙasa; yana da ministoci da gwamnoni da ke mara masa baya.”
“Ya kamata mu jira mu ga ko za a samu wani babban sauyi, in ba haka ba yanzu haka alamu na nuna shi ne ke da rinjaye, domin ban ga wani abu da zai hana shi samun nasara a zaɓe mai zuwa ba."
‘Ba mu fitar da ɗan takara ba,’ Tanko Yakasai
Alhaji Tanko Yakasai ya ce har yanzu ba a cimma matsaya ɗaya a tsakanin ‘yan siyasar Arewa kan zaɓen 2027 ba.

Asali: Facebook
Ya ce:
“Ban ji wani mutum daga ACF da ya fito fili ya faɗi ra’ayinsa game da zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba."
Yakasai ya ƙara da cewa ‘yan Najeriya su jira har sai shiyyar ta fitar da matsayarta a hukumance, ya kara da cewa rikice-rikicen cikin gida a jam'iyyu zai karawa Tinubu karfi.
"Kwankwaso na da zabi 3 a siyasa" - Salihu Yakasai
A baya, mun ruwaito cewa Salihu Tanko Yakasai, ya bayyana cewa akwai zaɓuɓɓuka uku kacal da suka rage wa jagoran jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, kafin babban zaɓen 2027.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu daga cikin magoya bayan Abdullahi Umar Ganduje ke ƙoƙarin dakile yiwuwar shigar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso cikin jam’iyyar APC.
Yakasai ya zayyana waɗannan zaɓuɓɓuka uku da ya ce su ne kawai hanyoyin da Kwankwaso zai iya bi domin ci gaba da kasancewa cikin sahun gaba a siyasar Najeriya, gabanin zaben 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng