Jam'iyyar PDP
Tsohon mai magana da yawun PDP, Kola Ologbondiyan ya yi ikirarin cewa gwamnoni da sauran ƴan siyasar da ke komawa APC mafutarsu kawai suke dubawa.
Wike ya nemi PDP ta kai tikitin 2027 Kudu. Ya ce ware tikitin 2023 zuwa Arewa ya haifar da rikici amma ana ganin Wike na kokarin hana Atiku takara a jam'iyyar ne.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa son rai ka iya karisa murkushe PDP tun kafin zaɓen 2027, yana mai cewa jam'iyyar ba za ta kai labari ba.
Saraki zai jagoranci kwamitin dinke barakar PDP. An ce kwamitin zai tabbatar da cewa an yi taron NEC da babban taron jam'iyyar cikin nasara don tunkarar 2027.
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya bayyana cewa jam'iyyun siyasa kamar APC da PDP ba su da bambanci domin duk manufarsu ɗaya a siyasar Najeriya.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana PDP a matsayin jam'iyyar da ta mutu murus. Ganduje ya ce Sule Lamido na hanyar shiga APC.
Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya fuskanci suka kan kalamansa game da tsarin jam’iyya ɗaya; NNPP da kungiyoyin farar hula sun yi watsi da ra’ayin.
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce nan gaba kadan shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje zai koma PDP idan APC ta wargaje kafin zaben 2027.
Bayan gwamnonin PDP sun maka Bola Tinubu a kotun koli kan dokar ta-ɓaci a Rivers, shugaban ya bukaci kotun koli ta yi watsi da karar da ke kalubalantarsa.
Jam'iyyar PDP
Samu kari