'Abin Kunya ne': An Buƙaci Bincike kan Zargin Cin Zarafin Minista Tuggar a Bauchi

'Abin Kunya ne': An Buƙaci Bincike kan Zargin Cin Zarafin Minista Tuggar a Bauchi

  • Wata ƙungiya ta matasan APC daga Bauchi ta buƙaci a gudanar da bincike kan zargin cin zarafin ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar
  • Kungiyar ta ce wani jami'in gwamnati ya ci zarafin ministan yayin ziyarar mataimakin shugaban ƙasa a bikin nadin sarauta a Bauchi
  • Matasan na APC sun bayyana cewa hakan na iya haddasa rikici a siyasa, tare da neman afuwa ga ma’aikatar harkokin waje da maslaha

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Wata ƙungiya mai suna 'APC Young Leaders Coalition' ta bukaci bincike kan zargin cin zarafin minista, Yusuf Tuggar.

Kungiyar da ke jihar Bauchi ta buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan lamarin tsakanin ministan da mataimakin gwamnan Bauchi, Auwal Jatau.

An dawo da maganar zargin cin zarafin ministan Tinubu a Bauchi
Kungiya ta bukaci bincike kan zargin ministan waje a Bauchi. Hoto: Yusuf Tuggar.
Asali: Facebook

Ana neman bincike kan cin zarafin minista

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da da shugaban ƙungiyar, Musa G. Khalid ya sanya wa hannu, cewar rahoton Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta damu da wani babban jami’in gwamnatin Bauchi da ake zargi ya dauki matakin saboda takaddama tsakaninsa da Gwamna Bala Mohammed.

Matasan sun ce abin da ya faru ba zai yiwu ba, ta nemi a gudanar da gaggawar bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru tsakanin su.

Sanarwar ta ce:

“Gwamnan Bauchi ko wani jami’insa ya ci zarafin minista, hakan babbar barna ce a tarihin siyasar jihar.
“Wannan dabi’ar jahilci ko kama da dabanci ya dace a bincika shi sosai domin gano gaskiyar abin da ya janyo hakan."
An gargadi gwamnatin Bauchi kan cin zarafin minista
Matasan APC sun buƙaci gwamnatin Bauchi ta ja kunnen ƴaƴanta kan cin zargin zarafin minista, Yusuf Tuggar. Hoto: Sen. Abdulkadir Bala Mohammed.
Asali: Facebook

Ana zargin ƴan PDP da haddasa rikici

Kungiyar ta zargi wasu 'yan PDP da haddasa rikicin da ya kai ga cin zarafi a filin jirgin sama na Sir Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Har ila yau, ta ce rahotanni sun tabbatar cewa wani babban jami’in gwamnati ya ci zarafin Ministan a gaban Mataimakin Shugaban Ƙasa, wanda ya nuna fushinsa.

Ƙungiyar ta ce idan PDP ba ta ɗauki matakin ladabtar da jami’anta ba, lamarin na iya rikidewa zuwa wani matsala mai haɗari.

Ta ce abin kunya ne irin wannan ya faru tsakanin abokan juna na dogon lokaci, Ambassada Tuggar da Gwamna Bala Mohammed.

Ta kara da cewa:

“Idan 'yan siyasa sun fara rashin da'a da rashin hakuri a gida, me zai hana su kai ga rikici a waje?
“Ya kamata a dakile wannan mummunan lamari tun da wuri, domin samun cigaba a jihar Bauchi.

Ƙungiyar ta ja kunnen gwamnatin jihar Bauchi da jami’anta da su daina ɗaukar matakan da za su iya wulakanta mambobin APC.

An ƙaryata labarin marin Ministan Tinubu

Kun ji cewa mataimakin gwamnan Bauchi, Mohammed Auwal Jatau, ya musanta zargin cewa ya mari ministan harkokin waje, Yusuf Maitama Tuggar.

Lamarin da ake cewa ya faru a cikin bas ya haddasa cece-kuce, inda wasu ke cewa rikici ya ɓarke kan lamarin siyasa.

Mai magana da yawun Jatau ya ce ba a taɓa samun hakan ba a Bauchi, yana ƙalubalantar masu da’awar da su kawo hujjoji.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.