Damagum: Shugaban PDP Ya Fadi Gwagwarmayar da za a Yi a Zaben 2027
- Shugaban PDP na riƙo, Umar Damagum, ya bayyana cewa makomar kasar nan na hannun 'yan Najeriya, musamman a lokacin zaben 2027
- Damagum ya yi kira ga masu zaɓe su yi amfani da 2027 wajen rama abin da gwamnatin APC ta yi masu, na jefa su a cikin kunci da wahala
- Kan sauya shekar jiga-jigan PDP zuwa APC, Damagum ya bayyana matukar takaici, ya ce jam'iyyar ba ta yi wa jagororin laifin komai ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja -A yayin da babban zaben 2027 ke kara karato wa, jam'iyyar PDP ta bayyana cewa zaɓen zai zama tsakanin talakawan Najeriya da gwamnatin APC.
Shugaban riko na PDP, Umar Iliya Damagum, ne ya bayyana haka a lokacin da ya mika takardar shaidar nasara ga Ezenwafor Jude, dan takarar jam'iyyarsa na zaben gwamnan Anambra mai zuwa.

Asali: Twitter
Punch News ta ruwaito cewa Ambasada Damagum ya ce, zaɓen 2027 ba wai zai nuna karfi ko yawan gwamnonin da wata jam'iyya ke da shi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce 'yan Najeriya za su zabi shugabansu ne, musamman bayan sun yi la'akari da halin da gwamnati mai ci ta jefa su a ciki.
PDP ta magantu kan matsalolin Najeriya
Aminiya ta ruwaito cewa shugaban PDP ya bayyana Najeriya a matsayin ƙasar da rayuwa ta yau da kullum ta zama kalubale ga talakawa.
Ya ƙara da cewa ya kamata masu kada kuri'a su kalli zaɓen a matsayin damar da za su ɗauka sama wa kansu saukin daga halin da suke ciki.

Asali: Twitter
Ya ce:
“Talaka yana jin zafi, kuma makoma na hannunsa. Don haka ina so in yi amfani da wannan dama in faɗa wa ’yan Najeriya cewa zaɓen nasu ne."
“Ba APC ce ta ke jayayya da kowanne gwamna ko sanata ko wani abu ba, sai APC na jayayya ne da ’yan Najeriya."
Damagum ya yi takaicin rasa 'yan PDP
A kan sauya shekar jiga-jigan jam'iyyarsa, Damagum ya nuna rashin jin daɗinsa, yana mai nuna damuwar saboda an rasa goyon bayan PDP ta ke ba jihar Delta PDP a shekarun baya.
Ya ce:
“Abin bakin ciki ne kuma abin alhinin gaske, saboda a ra'ayina, idan akwai wata jiha da ya kamata ta yi wannan tunanin, ba Delta ba ce, domin jam'iyyar ta kasance mai taimako sosai.
Ina gode wa Allah cewa a cikin sakon da suka aika, ba su ce jam'iyyar ta yi musu wani abu ba illa alheri.”
'Yan hadaka sun magantu kan gwamnonin PDP
A baya, kun ji cewa jigo a hadakar adawa da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ke jagoranta, Salihu Lukman ya ce ba su yi mamakin sauya shekar gwamnan Delta ba.
Ya bayyana cewa sun yi hasashen sauya shekar Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, da wanda ya gabace shi, Ifeanyi Okowa, da wasu manyan shugabannin jam’iyyar PDP.
Lukman ya kalubalanci sukar da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya yi wa Atiku Abubakar na cewa hadakar jam'iyyunsa ba za ta kai bantenta ba.
Asali: Legit.ng