Malami Ya Yi Hasashen Gwamnonin PDP 4 da Za Su Taya Tinubu Aiki a Zaɓen 2027
- Shugaban coci na INRI, Rabaran Elijah Ayodele, ya yi hasashen cewa gwamnoni hudu na PDP za su mara wa APC baya a zaben 2027
- Ayodele ya bayyana jihohin Akwa Ibom, Enugu, Oyo da Osun a matsayin wuraren da za a shawo kansu su sauya zuwa jam'iyyar APC
- Ya ce babu wani abu da ake kira kungiyar PDP yanzu, domin dukkan gwamnoni za su yi aiki ne da APC ba tare da shakka ba
- Malamin ya gargadi Tinubu da kada ya yi sakaci, yana mai cewa wasu mutane uku ya kamata su kau da kansu daga takara don nasara
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugaban cocin 'Evangelical Spiritual', Rabaran Elijah Ayodele ya magantu kan wasu gwamnonin PDP game da zaben 2027.
Malamin ya yi hasashe mai karfi dangane da zaben shugaban kasa na shekarar 2027 da ke tafe.

Asali: Twitter
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa ya fitar, malamin ya ambaci Akwa Ibom, Enugu, Oyo da Osun a matsayin jihohin da za a shawo kan su, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Sheriff ya koma APC daga PDP
A baya, rahoton Legit Hausa ya kawo muku labarin hasashen da ake game da wasu gwamnonin PDP da ke son komawa APC.
Akalla gwamnoni hudu na PDP na shirin sauya sheka zuwa APC, domin marawa shugaba Tinubu baya a yunkurinsa na zarce a 2027.
Gwamna Umo Eno ya bayyana cewa babu jam'iyya a Akwa Ibom yanzu, suna aiki tare da APC domin hadin kai da ci gaban kasa.
An ce Gwamna Frank Mbah da Sim Fubara suna nazarin marawa Tinubu baya ba tare da sauya sheka ba, yayin da wasu ke tattaunawa kan sauyin jam’iyya.
2027: Fasto ya yi hasashen zaben Tinubu
A cewarsa, gwamnoni hudu na PDP za su yi aiki da APC a zabe mai zuwa, wasu ma za su sauya sheka zuwa jam’iyyar mai mulki.
Ya ce:
“An riga an yi wa PDP da gwamnoni illa. Wasu za su koma APC kamar Akwa Ibom, Enugu, Anambra da Oyo za a shawo kansu; Osun ma haka.”
Ya kuma bayyana cewa jihar Anambra za ta kasance cikin tsarin shawo kai zuwa ga APC a shekarar 2027.

Asali: Facebook
Fasto ya gargadi Tinubu kan zaben 2027
Rabaran Ayodele ya kara da cewa an riga an rinjayi PDP, kuma babu wani amfani da kungiyar gwamnonin PDP ke yi yanzu.
Ya gargadi Shugaba Tinubu kada ya yi sakaci, inda ya fadi sunayen mutane uku da bai kamata su tsaya takara ba idan yana son nasara, cewar Daily Post.
A cewar limamin, Shugaba Tinubu yana bukatar daukar wasu matakai na musamman domin tabbatar da nasararsa a zaben 2027.
Gwamna Sheriff ya bar PDP zuwa APC
Kun ji cewa Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC a wani babban sauyin siyasa da ke ɗaukar hankula.
Gwamnan ya sanar da haka ne a wata ganawar sirri da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Asaba, tare da manyan shugabannin APC.
Sauyin jam’iyyar ya zo daidai lokacin da ake fuskantar sauye-sauye a siyasar jihar Delta, tare da shirye-shiryen zaɓen 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng