An Gano Yadda Gwamnonin PDP ke Takalo Rikici don Su Bar Jam'iyya

An Gano Yadda Gwamnonin PDP ke Takalo Rikici don Su Bar Jam'iyya

  • Dan majalisar PDP, Hon. Tajudeen Yusuf ya zargi wasu gwamnoni a PDP da haddasa rikici don su samu hujjar sauya sheka zuwa wata jam’iyya
  • Ya kara da cewe rikicin PDP ya samo asali ne tun bayan jam’iyyar ta kauce daga tsarin karba-karba da aka dora jam'iyyar a kai kafin zaɓen 2023
  • Tsohon dan majalisar ya bayyana cewa addini da kabilanci har yanzu na da tasiri wajen yanke shawara a gudanar da siyasar Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon dan majalisar wakilai, Tajudeen Yusuf, ya ce wasu gwamnoni a PDP na haddasa rikicin cikin gida domin su samu hujjar sauya sheka zuwa wata jam’iyya.

Hon. Yusuf ya ce matsalolin jam’iyyar sun tsananta ne bayan gazawarta wajen bin tsarin karba-karba da jam'iyyar ta fara kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Gwamnoni
Ana zargin gwamnonin PDP da haddasa rikici don su sauya sheka Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Twitter

Yusuf, wanda jigo ne a jam’iyyar PDP, ya bayyana hakan ne wata hira da ya yi da Sunrise Daily na talabijin na Channels a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'PDP ta sauka daga turba,' Hon. Yusuf

The Cable ta rawaito cewa Hon. Tajudeen Yusuf ya ce tun a shekarar 2023 ne PDP ta fara shiga cikin rikici bayan ta kauce daga manufofin da jam’iyyar ta ginu a kansu.

Ya ce:

“A shekarar 2023, mun kauce daga ainihin tsarin rabon mulki na shugabancin ƙasa da muka kafa tun farko.”
Shugaba
Mukaddashin shugaban PDP na kasa, Umar Damagum Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Facebook

Ya ƙara da cewa:

“Idan ka tuna, a shekarar 2014, mutane da dama sun yi korafi cewa Yar’Adua bai kammala wa’adinsa ba, kuma Goodluck Jonathan ya karɓa. A ra’ayin mutane da dama, Jonathan yana cin lokaci ne da ya kamata ya kasance na Arewa.”
“Gwamnoni biyar da Atiku Abubakar ke jagoranta sun fita daga taron jam’iyyar da aka yi a Eagle Square — wannan ne farkon rikicin PDP.”

“Yadda siyasar 2027 za ta kasance”

Tsohon dan majalisar da ya wakilci mazabar Kabba/Bunu/Ijumu a jihar Kogi na tsawon shekaru 12 ya ce har yanzu kabilanci da addini na taka muhimmiyar rawa wajen yanke shawarar siyasa a Najeriya.

Hon. Yusuf ya ce:

“A halin yanzu, ba za a iya raba siyasar Najeriya da kabilanci da addini ba. Wata rana za mu kai ga hakan, amma yanzu ba haka abin yake ba.”

Ya tunatar da cewa a shekarar 2019, dukkan ‘yan takarar shugaban ƙasa na PDP sun fito ne daga Arewa, amma a shekarar 2022, wasu ‘yan takara daga kudu sun fara neman kujerar.

Hadakar Atiku ta soki gwamnonin PDP

A wani labarin, mun wallafa cewa hadakar siyasa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ke jagoranta ya caccaki gwamnonin PDP bisa zargin ƙwace ikon da jam'iyyar.

Salihu Mohammed Lukman, mai magana da yawun hadakar, ya bayyana cewa tafiyar Atiku ita ce mafita ga Najeriya, kuma hadakar za ta iya doke jam’iyyar APC da Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Lukman ya zargi wasu daga cikin gwamnonin PDP da yin aiki a asirce da gwamnatin Tinubu domin hana kafuwar cikakkiyar adawa, yana mai cewa hakan babban barazana ce.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.